Gwamnan Jihar Borno Ya Kara Wa'adin Shekarun Ritayar Ma'aikatan Lafiya Zuwa Shekara 65

Gwamnan Jihar Borno Ya Kara Wa'adin Shekarun Ritayar Ma'aikatan Lafiya Zuwa Shekara 65

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Zulum, ya amince da ƙara wa'adin shekarun ritayar ma'aikatan lafiya a jihar
  • Gwamnan ya ƙara wa'adin shekarun aikin ƙafin yin ritaya daga shekara 35 zuwa 40 ko shekara 65 da haihuwa
  • Tun a baya gwamna Zulum ya ƙara wa'adin shekarun aiki na malaman makaranta a jihar zuwa shekara 40 na aiki ko shekara 65 da haihuwa

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta sanar da ƙara wa'adin shekarun ritayar ma'aikatan lafiya na jihar daga shekara 35 zuwa 40 suna aiki ko 65 da haihuwa.

Jaridar The Cable tace darektan ma'aikatar lafiya a matakin farko Ibrahim Sheriff, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikewa shugabannin ƙananan hukumomin jihar.

Gwamna Zulum ya kara shekarun ritayar ma'aikatan lafiya
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

A cikin sanarwar Sheriff ya bayyana cewa ƙarin wa'adin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2022.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna APC Ba Shi Da Lafiya, Ya Miƙa Mulki Ga Mataimakinsa Ya Tafi Ƙasar Waje Ganin Likita

Ma'aikatan da suka yi ritaya za su iya dawowa bakin aiki

Sheriff ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta kuma amince ma'aikatan lafiyan da suka yi ritaya kafin ko bayan ranar 1, ga watan Janairun 2022, za su iya dawowa bakin aiki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar da darektan ya fitar na cewa:

"Gwamnan jihar Borno, mai girma Babagana Umara Zulum, min, FNSE, CON, ya amince da ƙara wa'adin shekarun aiki na ma'aikatan lafiya daga shekara 35 zuwa 40 suna aiki ko shekara 65 da haihuwa, wanda ya fara daga ranar 1, ga watan Janairun, 2022."
"Haka kuma duk waɗanda suka yi ritaya kafin ko bayan ranar 1, ga watan Janairun 2022, ana buƙatar su dawo bakin aiki idan suna ra'ayi."

Tun da farko gwamna Zulum ya ƙara wa'adin shekarun ritaya na malaman makaranta a jihar zuwa shekara 65 na haihuwa ko shekara 40 suna aiki.

Kara karanta wannan

Mazan Fama: Sojoji Sun Kai Samame Sansanin 'Yan Bindiga, Sun Sheƙe da Dama a Musayar Wuta

Tinubu Zai Duba Yiwuwar Tsawaita Wa'adin Dena Amfani Da Tsaffin Naira

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na duba yiwuwar sake ƙara wa'adin amfani tsaffin kudaɗe a ƙasar nan zuwa watan Disamban shekarar 2024.

Shugaban ƙasar na duba yiwuwr hakan ne bayan shawarar da wani kwamiti da ya kafa ya bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng