Wani Mutum Da Danginsa Suka Yanke Zumunci Da Shi Ya Yi Karyan Ya Mutu, Ya Bayyana a Wajen Jana'izarsa

Wani Mutum Da Danginsa Suka Yanke Zumunci Da Shi Ya Yi Karyan Ya Mutu, Ya Bayyana a Wajen Jana'izarsa

  • Wani mutum mai suna David Baerten ya shiga damuwa bayan danginsa gaba daya sun yanke zumunci da shi
  • Domin koya masu darasi a kan rayuwa da muhimmancin zumunci, sai ya yi karyan cewa ya mutu
  • Sai dai, ana tsaka da zaman makokinsa, sai ga Baerten ya bayyana a wajen tare da bayyana dalilinsa na aikata haka

Wani mutumin Belgium mai shekaru 45, David Baerten, ya yi karyan ya mutu sannan ya isa wajen jana’izarsa a cikin jirgi mai saukar ungulu domin koyawa danginsa darasi kan muhimmancin zumunci.

Baerten, wanda ke watsa shirye-shirye a TikTok, ya sanarwa matarsa da yara shirinsa, inda su kuma suka taimaka masa ta hanyar watsa shi a soshiyal midiya.

Taron jana'izar karya
Wani Mutum Da Danginsa Suka Yanke Zumunci Da Shi Ya Yi Karyan Ya Mutu, Ya Bayyana a Wajen Jana'izarsa Hoto: The Independent
Asali: UGC

Daya daga cikin yaran Baerten ta yaudari mabiya shafin mahaifinta cewa ya mutu ta hanyar rubuta:

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Rayuwa Babu Ita Ba”: Dan Najeriya Ya Yi Wuff Da Tsohuwar Baturiya, Hotunan Su Yadu

"Allah ya ji kanka, mahaifina. Ba zan taba daina tunaninka ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Me yasa rayuwa bata da adalci? Me yasa sai kai? Za ka zama kaka, sannan kana da gaba daya rayuwarka a gabanka. Ina kaunarka! Muna kaunarka! Ba za mu taba mantawa da kai ba.”

Iyalin sun shirya jana'izarsa, sannan da masu juyayi suka taru, sai Baerten ya isa a jirgi mai saukar ungulu da tawagar masu daukar bidiyo.

A daya daga cikin bidiyon, an gano wani dangi baerten rungume da shi suna sharban kuka yayin da mutane suka tare a wajen.

Dalilin da yasa na yi karyan na mutu, Baerten

Baerten ya yi bayanin dalilinsa na aikata abun da ya yi, yana mai cewa yana son ganin yadda daginsa za su yi bayan ya bayyana cewa sun yanke hulda da shi.

Kara karanta wannan

Jarumi Kuma Mutum Mafi Tsawo a Najeriya, Afeez Agoro, Ya Rasu

Ya ce:

“Abun da nake gani a dangina yana matukar kona mun rai. Ba a taba gayyatana zuwa wani abu ba. Babu wanda ke ganina. Duk mun rabu. Ina ji kamar ba a sona.
“Wannan ne dalilin da yasa na so koya masu darasi a rayuwa sannan na nuna masu cewa kada su jira sai mutum ya mutu kafin ya hadu da su.”

Kalli bidiyoyin a kasa:

Dan Najeriya ya hana fasinjoji sauka daga jirgin sama saboda ya nemi jakar kilishinsa ya rasa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan Najeriya ya haddasa yar dirama inda ya hana fasinjojin jirgin sama sauka bayan sun isa filin jirgin da za su sauka.

Mutumin dai ya nemi jakar da ya yi guzirin kilishi ya rasa lamarin da ya fusata shi har ya kai ga neman kowa ya binciki kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng