Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Abdulsalam Abubakar a Villa

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa Da Abdulsalam Abubakar a Villa

  • Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Abdulsalam Abubakar, ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja
  • Abdulsalam Abubakar wanda shi ne tsohon shugaban na ƙasa biyu da ya ziyarci Tinubu tun bayan hawansa mulki, ya kai ziyarar ne a ranar Alhamis
  • A ranar Talata, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaba Tinubu, inda ya yi masa bayanin halin da ake ciki a yankin Afirika ta Yamma

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja.

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa a cikin wani bidiyo da tashar talbijin ta Nigeria Television Authority (NTA) ta sanya, ya nuna lokacin da Abdulsalami ya iso, inda Shugaba Tinubu yana wajen domin tarbarsa bayan ya sauko daga mota.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunaye: Shugaba Tinubu Ya Naɗa Nuhu Ribaɗo da Wasu Mutum 7 a Manyan Muƙamai

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da Abdulsalam Abubakar
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Dukkanin shugabannin sun yi raha tare da hadimansu kafin daga bisani suka wuce ofishin shugaban ƙasa, domin gudanar da taron su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗanne batutuwa za su tattauna a taron?

Makasuɗin dalilin ganawar shugabannin biyu bai fito ba, har ya zuwa lokacin fara tattaunawar ta su.

Kafin zuwan Abulsalami, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) wacce mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranta.

Abdulsalami shi ne tsohon shugaban ƙasa na biyu da ya gana ido da ido da Shugaba Tinubu tun bayan da ya ɗare kan madafun ikon mulkin ƙasar nan.

A ranar Talata, shugaban ƙasar ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a fadarsa da ke Villa a Abuja. A lokacin taron na su, Jonathan ya yi wa Shugaba Tinubu bayani kan halin da ake ciki a yankin Afirika ta yamma.

Kara karanta wannan

Ta Bayyana: Dalilin Da Yasa Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa

Idan ba a manta ba dai, Abdulsalam Abubakar shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na ƙasa, wanda yake da alhakin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ƴan takara a lokacin zaɓe, musamman na shugaban ƙasa.

Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Tsohon Sarkin Kano

A wani labarin kuma, shugaba Tinubu ya sanya labule da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Ganawar ta su ita ce ta farko tun bayan da shugaban Tinubi ya hau kan mulkin ƙasar nan a ƙarshen watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng