Yanzu Yanzu: Mutum Mafi Tsawo a Najeriya, Afeez Agoro, Ya Rasu

Yanzu Yanzu: Mutum Mafi Tsawo a Najeriya, Afeez Agoro, Ya Rasu

  • Mutum mafi tsawo a Najeriya kuma jarumin Nollywood, Afeez Agoro Oladimeji, ya kwanta dama
  • Matashin ya rasu ne a daren ranar Laraba, 15 ga watan Yuni bayan ya yi fama da rashin lafiya
  • Labarin mutuwarsa ya bugi masoyansa a soshiyal midiya inda da dama suka yi zantuka game da mutuwarsa

Shahararren jarumin fim, Afeez Agoro Oladimiji, wanda aka fi sani da mutum mafi tsawo a Najeriya ya rasu.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa tuni aka fara shirye-shiryen sada Agoro da gidansa na gaskiya a gidansa da ke hanyar cikin gari, Akoka.

Mutumin da ya fi kowa tsawo a Najeriya
Yanzu Yanzu: Mutum Mafi Tsawo a Najeriya, Afeez Agoro, Ya Rasu Hoto: @seunoloketuyi
Asali: Instagram

An tattaro cewa an kwashi Agoro zuwa asibiti a ranar Laraba, 14 ga watan Yuni bayan ya shiga wani yanayi na rashin lafiya.

An yi wa Agoro tiyata a kwankwaso

Wallafar karshe da marigayin ya yi a shafinsa na Facebook ya kasance a ranar 28 ga watan Mayu bayan ya farfado daga aikin sauya kwankwaso da akayi masa.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Kai Kara Wajen EFCC, Ya Ce Tsohon Gwamna Ya Karkatar da N1tr

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya wallafa a shafin nasa:

"Godiya ga Allah madaukakin sarki kan tiyata mai cike da nasara yanzu lokacin yin magani ne."

Agoro ya farfado daga aikin da aka yi masa a kwankwaso da taimakon likitansa Dr Dike.

Kafin mutuwarsa, tsawon da Allah ya yi wa Agoro mai ban tsoro na jan hankalin mutane a duk inda ya shiga. Tsawonsa ya kai sahu 7 da digo 4.

Al'ummar Akoka/Bariga sun fara aika sakonninsu na ta'aziyya.

Shugaban yankin Akoka, Segun Adesanya ya tabbatar da mutuwar nasa.

Ya ce:

"Afeez Agoro yana zaune ne a hanyar cikin gari kuma abun bakin ciki ne mun rasa jajirtaccen matashi. Allah ya ji kansa da rahama."

Jama'a sun yi martani kan mutuwar Agoro

Nan take labarin mutuwar Agoro ya yadu a soshiyal midiya inda yan Najeriya da dama suka tofa albarkacin bakunansu. Wasu sun caccaki mutanen da basu taimaka masa ba lokacin da yake rashin lafiya.

Kara karanta wannan

“Rashawa Kiri-Kiri”: Babban Lauya Ya Caccaki Tsohon Sanata Kan Sakin Bakin Da Ya Yi a Zauren Majalisar Dattawa

Karanta wasu daga cikin martanin a kasa:

hollando___:

"Ya shafe watanni yana rokon jama'a su taimaka masa. A karshe ya samu zaman lafiya."

official_wendy__:

"Chaiiii sun kasa taimakawa mutumin nan sannan haka ya mutu kawai....Allah ya ji kansa."

amure_13:

"Lokacin da mutumin nan ke neman kudi don ayi masa aikin sauya kwankwaso, duk baku taimaka wajen wallafa shi ba fa! Yanzu ya mutu duk kuna yayata shi...rayuwa...."

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo ya rasu

A wani labarin kuma, mun ji cewa al'ummar Imo na cikin alhini yayin da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dr Douglas Acholonu, ya kwanta dama.

Acholonu wanda ya kasance kwararren likita ya mutu a ranar Lahadi, 4 ga watan Yuni kuma za a binne shi a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng