Yanzu Yanzu: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Jigon PDP a Akwa Ibom
- Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da wani babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Akwa Ibom a ranar Litinin
- Masu garkuwa da mutane sun sace Cif Eyo Edet cikin wata motar Sienna a gidan mansa da ke karamar hukumar Oron ta jihar kafin suka saka shi cikin jirgin ruwa
- Rundunar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce ta kaddamar da bincike don gurfanar da mutanen
Akwa Ibom - Wasu mutane da ake zaton yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Akwa Ibom, Cif Eyo Edet.
Jaridar Punch ta rahoto cewa an yi garkuwa da Edet wanda aka fi sani da Eyo Aswang, a ranar Litinin a gidan mansa mai suna Eyotech Nigeria Limited, a karamar hukumar Oron da ke jihar.
Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka
Wata majiya ta bayyana a ranar Talata cewa masu garkuwa da mutane ne suka kama Edet wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin jagoran kungiyar yakin neman zaben PDP a Oron a zaben da ya gabata, sannan suka yi awon gaba da shi a wata mota kirar Sienna.
Maharan sun saka shi a jirgin ruwa sannan suka kona motarsu
Majiyar ta kuma bayyana cewa maharan sun kai jigon siyasar zuwa cikin wani jirgin ruwa da ke jiransu sannan suka cinnawa motar da ta kaisu wajen wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Post ta nakalto wani ganau yana cewa:
"Yana nan a gidan mansa lokacin da wadannan yaran suka zo sannan suka ja shi zuwa cikin motarsu kirar Sienna suna ta harbi ba kakkautawa a iska, sun tafi da shi zuwa wani wuri sannan suka saka shi a wani jirgin ruwa da ya kwaso gudu suka kuma sanyawa motar wuta."
Har zuwa lokacin kawo wannan rahoton, maharan basu tuntubi danginsa don neman kudin fansa ba.
Rundunar yan sanda ta yi martani
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Odiko Macdon, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce kwamishinan yan sandan jihar, CP Olatoye Durosinmi ya ziyarci wajen faruwar abun sannan ya yi umurnin gudanar da bincike kan lamarin.
Macdon ya ce:
"Mun samu labarin, kwamishinan yan sanda, CP Olatoye Durosinmi ya ziyarci wajen da abun ya faru kuma ya je a bakin ruwan hatta da motar Sienna da maharan suka yi amfani da shi an gano shi.
"An fara gudanar da bincike kuma ina da tabbacin za a gurfanar da maharan nan ba da jimawa ba."
Yan bindigar sun farmaki al'ummar jihar Neja, sun kashe manoma da dama
A wani labari na daban, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun farmaki garuruwa daban-daban a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.
An rahoto cewa yan bindigan sun kai hare-haren ne tsakanin ranar Laraba da Asabar inda suka kashe mutane masu yawan gaske.
Asali: Legit.ng