Matan Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Sun Yi Kokarin Ba Hammata Iska a Zauren Majalisa

Matan Sabon Kakakin Majalisar Wakilai Sun Yi Kokarin Ba Hammata Iska a Zauren Majalisa

  • Matan sabon kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, sun janyo abin magana a dandamalin zauren majalisar wakilai
  • Matan sai sun so su ba hammata iska ana cikin rantsar da shi bayan da ɗaya daga cikinsu ta ture kishiyarta daga gefensa
  • Hakan ya sanya an samu tsaiko wajen rantsuwar inda har sai da Alhassan Doguwa ya sanya baki rikicin ya lafa

FCT, Abuja - An ɗan samu hargitsi a majalisar wakilai a tsakanin matan sabon kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen a ranar Talata.

Lamarin ya auku ne lokacin da sabon kakakin majalisar yake yin rantsuwar kama aiki, inda matan suka nemi ba hammata iska a dandamalin majalisar, cewar rahoton The Cable.

Matan Abbas Tajudeen sun yi hargitsi a zauren majalisa
Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Hakan na zuwa ne bayan Tajudeen Abbas ya samu nasarar lashe zaɓen kakakin majalisar da tazara mai nisa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: APC Ta Rasa 1, Gbaja Ya Yi Murabus Daga Majalisar Wakilan Tarayya

Komai yana tafiya daidai lokacin da aka kira Abbas zuwa kan dandamalin majalisar domin ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon kakakin majalisar wakilai ta 10.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamoru Ogunlana, mataimakin magatakardan majalisar shi ne ya karanto kalmonin rantsuwar domin sabon kakakin majalisar ya maimaita.

Matan sun yi hargitsi a zauren majalisa

Abbas yana tare da ɗaya daga cikin matansa a ɓangaren dama, yayin da Alhassan Doguwa ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa/Tudun yake a ɓangaren hagunsa.

Sai dai ana cikin rantsuwar kawai sai ɗayar matar Abbas ta zo ta kawo hargitsi inda ta ture ɗayar matar daga gefen sabon kakakin majalisar.

Abinda ta yi ya yi matuƙar ba Abbas mamaki, wanda sai da ya dakatar da rantsuwarsa ya bulbuleta da faɗa kan abin kunyar da ta aikata.

Alhassan Doguwa ne ya sanya baki inda ya ba ɗayar matar da aka ture baki, sannan ya matsa mata ta dawo gefen Abbas na hagu domin ƙura ta lafa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Femi Gbajabiamila Ya Shirya Yin Murabus, Bayanai Sun Fito

Ga bidiyon nan ƙasa:

Majalisar Wakilai Ta Yi Sabon Kakaki

A wani labarin, kun ji yadda majalisar wakilan tarayyar Najeriya taa zaɓi sabon kakakinta wanda zai ja ragamar majalisar nan da shekara huɗu masu zuwa.

Abbas Tajudeen ɗan majalisar wakilai daga Zaria a jihar Kaɗuna, shi ne ya samu nasarar zama sabon kakakin majalisar wakilai ta 10.

Tajudeen ya doke abokan takararsa Wase da Jaji inda ya basu ƙuri'u masu yawa a zaɓen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng