Wani Matashi Da Ke Gab Da Yin Aure Ya Rasa Ransa Sakamakon Nutsewa A Ruwa A Enugu

Wani Matashi Da Ke Gab Da Yin Aure Ya Rasa Ransa Sakamakon Nutsewa A Ruwa A Enugu

  • Ambaliyar ruwa sakamakon matsanancin ruwan sama, ta yi sanadiyyar nutsewar wani matashi mai suna Chukwudi cikin ɗakinsa a jihar Enugu
  • Chukwudi dai ya gama duk al'adunsu na gargajiya na shirye-shiryen bikin aurensa da yake ƙaratowa
  • Gidan ya kasance ne a kan hanyar ruwa, wanda hakan kan janyo musu ambaliyar sakamakon toshe hanyarsa da aka yi

Enugu - Ambaliyar ruwan da aka yi a daren Lahadin da ta gabata, ta yi sanadiyyar nutseear wani matashi mai suna Chukwudi a gidan da yake kwana.

Gidan ya kasance kusa da wata ‘yar karamar magudanar ruwa a garin Ogui, da ke jihar Enugu.

Vanguard ta ruwaito cewa, matashin ya riga da ya yi duk al'adun gargajiya da ake yi na shirin bikin aurensa a lokacin da mummunan lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

“Guba Wani Ya Saka Musu A Abinci” An Tsinci Gawar Mata Da Miji Kwance Cikin Gidansu A Abuja

Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar matashi a Enugu
Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar rasuwar wani matashi da ke shirin aure a Enugu. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An gina gidan ne a kan hanyar da ruwa ke wucewa

Rahoton ya bayyana cewa, gidan da Chukwudi yake zaune a lokacin da lamarin ya faru, yana yawan fuskantar ambaliya tun shekaru shida nan baya.

Rahoton ya ce an gina gidan ne a kan hanyar da ruwa ke wucewa zuwa wani rafi da ake cewa rafin Asata.

A cewar wata shaidar gani da ido, wacce ita ma tana haya ne a gidan mai suna Misis Nkechi Eze, a ranar Litinin ta makon da ya gabata ma sun fuskanci malalowar ruwa cikin gidan, inda sai da suka kwashe kayansu.

Ta ƙara da cewa a wancan karan ba a samu asarar rai ko ɗaya ba, sai dai ɓarna da ruwan ya yi, wanda daga lokacin ne shi marigayin ya daina kwana a gidan shi da budurwar tasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Ci Gaba Da Aikin Rusau Bayan Zazzafan Musayar Yawu Da Aka Yi Tsakanin Ganduje Da Kwankwaso

Yadda matashin ya nutse a ruwan

Nkechi ta bayyana cewa, matashin ya zo tare da budurwarsa domin su duba kayayyakinsu, kwatsam sai ga ruwa ya zo.

Ta ce Chukwudi ne ya riƙa shelantawa mutane cewa ga fa ruwa nan ya dawo.

Sai dai a yayin da kowa ke ƙoƙarin janye jikinsa, shi marigayin sai ya kutsa kai cikin ɗakin nasa da zummar ya ɗebo wasu kayayyaki.

A cewarta:

“Tunda ya shiga shikenan bai fito ba. Wata yarinya kurma da ke zaune a ɗaya daga cikin ɗakunan a ta kusa nutsewa, amma mutane sun yi nasarar ceto ta.”

Nkechi ta kuma bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun iso da misalin ƙarfe 12 na dare, inda suka fara ƙoƙarin kwashe ruwan da ya cika gidan.

Ta ƙara da cewa sun yi amfani da injin janye ruwa, wanda sai ƙarfe 5 na safe aka samu nasarar gano gawar matashin.

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa a 2022, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa Ta Ƙasa (NEMA), ta koka kan yawaitar ambaliyar da aka samu a shekarar.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Yadda wata matar aure ta haifi yara huɗu tare da surukinta

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun karanta labarin wata mata da ta haifi yara har guda huɗu tare da surukinta.

Matar wacce a yanzu abin ke damunta, ta bayyana cewa ta gano cewa mijin na ta ba zai iya haihuwa bane, shi ya sa ta yi wannan ɗanyen aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng