"Kai Makaryaci Ne": Dan Majalisa Ya Caccaki Ministan Buhari, Ya Bayyana Dalilansa

"Kai Makaryaci Ne": Dan Majalisa Ya Caccaki Ministan Buhari, Ya Bayyana Dalilansa

  • Nnolim Nnaji, tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama, ya yi martani mai zafi kan Hadi Sirika
  • A cewar Nnaji, tsohon ministan sufurin jiragen saman na gwamnatin Buhari, ƙarya yake masa saboda ya buƙaci ayi abinda ya dace
  • Kalaman Nnaji martani ne kan zargin da tsohon ministan ya yi na cewa ya nemi cin hancin kaso 5% na kamfanin jirgin saman Najeriya

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin jiragen sama, Nnolim Nnaji, ya caccaki tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, saboda jifarsa da ƙarya.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ɗan majalisar ya bayyana hakan ne a martanin da ya yi kan zargin da tsohon ministan ya yi masa.

Dan majalisa ya caccaki Hadi Sirika
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika Hoto: Hadi Sirika
Asali: Facebook

Sirika a cikin wata tattaunawa da tashar talbijin ta Arise TV a ranar Lahadi, 11 ga watan Yuni, ya yi zargin cewa ɗan majalisar ya buƙaci da a ba shi kaso 5% na jirgin saman Najeriya.

Kara karanta wannan

Batun jirgin Nigeria Air: Hadi Sirika ya tono asiri, ya ce dan majalisa ya nemi cin hanci

A kalamansa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hon Nnaji ya nemi da na ba shi kaso 5% na jirgin saman Najeriya domin shi da mutanensa."

Da yake mayar da martani a ranar Lahadi, ɗan majalisar ya bayyana cewa tsohon ministan ƙarya kawai yake yi masa saboda ya haƙiƙance cewa sai an yi abinda ya dace, cewar rahoton The Punch.

Nnaji ya caccaki ministan Buhari kan zargin cin hanci

Ya bayyana Hadi Sirika a matsayin wanda ya kusa nutsewa, inda ya ƙara da cewa yana ƙoƙarin tsira ne daga caccakar da yake sha tun bayan ƙaddamar da jirgin saman Najeriya a ƙarshen wa'adin mulkin Shugaba Buhari.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa bai kamata ya yi martani kan zargin da ya yi masa ba, amma akwai buƙatar ya yi hakan saboda mutanensa da ƴan Najeriya.

"Sirika mutum ne wanda ya kusa nutsewa inda ya ke neman abokin mutuwa domin ya tsira daga caccakar da yake sha tun lokacin da ya ƙaddamar da jirgin saman Najeriya." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Ta Fusata, Ta Yi Martani Mai Zafi Kan Ganduje Bisa Barazanar Marin Kwankwaso

Sirika Ya Tona Asirin Dan Majalisa

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa tsohon ministan harkokin sufurin jirahen sama, Hadi Sirika, ya zargi ɗan majalisar da ya fara kushe jirgin saman Najeriya da neman cin hanci a wajensa.

Sirika ya bayyana cewa ɗan majalisar ya nemi da ya bashi kaso 5% na jirgin saman Najeriya, domin ya raba da shi da mutanensa.

Ɗan majalisar dai ya kushe jirgin saman Najeriya inda ya kira shi da yaudara ce kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng