Karin Makarantu: Hukumar NUC Ta Amince da Kafa Jami’o’i Masu Zaman Kansu 37 a Najeriya

Karin Makarantu: Hukumar NUC Ta Amince da Kafa Jami’o’i Masu Zaman Kansu 37 a Najeriya

  • Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta ba da lasisin wucin gadi ga sabbin jami’o’i 37 masu zaman kansu
  • Sakataren zartarwa na NUC, Farfesa Abubakar Rasheed ya bukaci masu jami’o’in da kada su yi tsammanin samun wani tukuicin kudi daga jarin da suka zuba a fannin ilimi
  • Rasheed ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kafa jami’o’in 37 a ranar 15 ga watan Mayu

FCT, Abuja Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta bukaci masu jami’o’i masu zaman kansu da kada su yi tsammanin samun tukuicin kudi saboda kafa manyan makarantu a kasar nan.

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, babban sakataren hukumar ta NUC, Farfesa Abubakar Rasheed ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayyana samar da lasisin wucin gadi ga sabbin jami’o’i 37 masu zaman kansu a Najeriya.

Kara karanta wannan

DSS Ta Jero 'Laifuffukan' Emefiele, Za Ta Bukaci Karin Lokacin Cigaba da Tsare Shi

Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta amince da kafa jami’o’in 37 a ranar 15 ga watan Mayu.

NUC ta amince a kafa sabbin jami'o'i a Najeriya
Hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) | Hoto: National Universities Commision
Asali: Depositphotos

Ba a neman kudi da sunan kafa jami’a a Najeriya, inji NUC

Rasheed ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“A fannin kafa jami’o’i, ba kun yi hakan ne don tsammanin samun tukuicin kudi ba. Idan babban dalilinku shine samun kudi, to kun zo a wurin da bai dace ba. Kuna kafa jami’a ne don ba kasa gudunmawa.
"Kafa jami'o'i masu zaman kansu yana matukar bukatar sha’awa da ra’ayi ne na mutum, don haka sha'awarce ya kamata ta motsa ku."

Bukatar karatun gaba da sakandare a Najeriya

Ya bayyana tsananin bukatar shiga jami’a da ake samu da kuma karuwar daliban da suka kammala karatun sakandare, wanda ya sanya samun damar shiga jami’a ya zama kalubale a kasar nan.

A cewar Rasheed, samun ilimun manyan makarantu ya kasance wani ginshikin gini da bunkasa jarin dan Adam a kasar nan.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

Yace:

“Kididdigar Najeriya na yawan masu ilimin manyan makarantu bai wadata sosai ba. Kididdiga ta nuna cewa adadin wadanda suka shiga manyan makarantu ya kai miliyan 2.23 wanda shine kusan 12% cikin 100% na adadin mutane miliyan 220.”

Tinubu zai shiga matsala, ‘yan kwadago za su fara yajin aiki

A wani labarin, yayin da ba a gama da batun ASUU da sauran kungiyoyin jami’o’I ba a Najeriya, kungiyar kwadago za ta shilla yajin aiki.

Yajin aikin na da nasaba da yadda sabon shugaban kasar Najeriya ya bayyana janye tallafin man fetur daga karbar mulkin kasar.

Ya zuwa yanzu, ana sauraran abin da ASUU za ta fara bayyanawa bayan da Tinubu ya karbi ragamar kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.