Gwamnan Jihar Benue Ya Kafa Kwamitin Kwato Kadarorin Gwamnatin Jihar Da Aka Sace

Gwamnan Jihar Benue Ya Kafa Kwamitin Kwato Kadarorin Gwamnatin Jihar Da Aka Sace

  • Gwamnatin jihar Benue ta shirya ƙwato dukkanin kadarorin gwamnatin jihar da aka sace a gwamnatin baya da ta gabace shi
  • Gwamnan jihar Rev. Fr. Hyacinth Alia ya kafa kwamitocin da za su yi aiki wajen ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da suka yi ɓatan dabo
  • An ɗorawa kwamitocin alhakin bi lungu da saƙo domin ƙwato duk wata kadara ta gwamnati da aka yi awon gaba da ita

Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benue ta Hyacinth Ali ta kafa kwamitin ƙwato kayayyakin gwamnati da gwamnatin magabacinsa ta sace, cewar rahoton Punch.

A kwanakin baya gwamnan jihar ya koka kan satar motocin gwamnati da gwamnatin da ta gabacesa a ƙarƙashin Samuel Ortom, ta yi.

Gwamnan Benue ya kafa kwamitin kwato kadarorin gwamnati
Gwamnan jihar Benue, Rev. Fr. Hyacinth Alia Hoto: Thenigerialawyer.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Tersoo Kula, ya fitar ya bayyana cewa gwamnan ya kafa kwamitin kwato kadarorin gwamnatin a matakin jiha da na ƙananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Ashsha: Matawalle Ya Bayyana Irin Satar Da Gwamnatin Zamfara Ta Yi Masa a Gida Da Sunan Kwacen Motoci

Gwamnati ta yi sanarwa

Sanarwar ta bayyana cewa an ɗorawa mambobin kwamitocin alhakin gano yawan kadarorin gwamnati da aka yi ciki da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Gwamnan jihar Benue, Rev. Fr. Dr. Hyacinth Alia ya ƙaddamar da kwamitocin ƙwato kadarori guda biyu. Ɗaya zai yi aiki a matakin jiha yayin da ɗayan zai yi aiki a matakin ƙananan hukumomi."
"Daga cikin ayyukan mambobin kwamitin an ɗora musu alhakin ƙwato kadarorin gwamnati da suka haɗa da filaye, motoci, gidaje, kayan ɗaki da sauransu."

A cewar sanarwar za a haɗa mambobin kwamitin da jami'an tsaro domin ƙwato kadarorin gwamnatin, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A matakin jiha tsohon babban sakatare, Hingah Biem shi ne shugaban kwamitin, sauran mambobin kwamitin sun haɗa da, Barr. Joe Abaagu, Dennis Akura Ioryue Yajir, Peter Egbodo,Joseph Ojob, Jonathan Modi, Shaageer Matins, Yuhe Jerome, Tom Uja da Tormbuwua Terlumun a matsayin mamba kuma sakatare.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Niger Ya Rantsar Da Sakataren Gwamnatin Jihar Da Wasu Muhimman Mukamai Da Ya Nada

A matakin ƙananan hukumomi mambobin kwamitin sun haɗa da, Jude Tyo, Aondowase Apera, Kwaghgba Amande, Richard Dzungweve, Anthony Sende, Olofu Ogwuche, Terver Kachina, da Nick Eworo a matsayin mamba kuma sakatare.

Gwamna Ya Karbe Filin da Aka Ba Jami’ar Janar Ibrahim Babangida

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Niger ya ƙwace filin da aka mallakawa jami'ar Ibrahim Babangida (IBB) da ke a Suleja.

Muhammad Umar Bago ya kuma ƙwace takardun mallaka na wasu kamfanonin da aka bayar a baya. Hakan na zuwa bayan gwamnan ya rattaɓa hannu kan wata sabuwar doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng