Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bayyana Inda Ya Samo Motocin Da Jami'an Tsaro Suka Kwace

Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bayyana Inda Ya Samo Motocin Da Jami'an Tsaro Suka Kwace

  • Bello Matawalle tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce shi ba mai yunwar motoci bane tun kafin ya zama gwamnan jihar
  • Matawalle ya ce da yawa daga cikin motocin da aka kwaso a gidajensa ya mallakesu ne tun kafin ya zama gwamnan jihar
  • Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa jami'an tsaron gaban kansu suka yi domin ba wanda ya sanar da shi a hukumance za a shigar masa gidaje

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa yana da arziƙin motoci tun kafin ya zama gwamnan jihar Zamfara.

Jaridar Channels tv ta ambato tsohon gwamnan na cewa mafi yawa daga cikin motocinsa da jami'an tsaro suka kwashe a gidajensa guda biyu na Gusau da Maradun, ya siyosu ne tun kafin ya zama gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Jami'an Tsaro Suka Mamaye Dakataccen Gwamnan CBN a Filin Jirgin Sama

Matawalle ya bayyana inda ya samo motocinsa
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle Hoto: Bbchausa.com
Asali: UGC

Matawalle yana mayar da martani ne bayan jami'an tsaron ƴan sanda da ƴan sandan farin kaya sun sun kai sumame gidajensa ranar Juma'a.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa da yawa daga cikin motocin ya siyosu ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna a jihar, cewar rahoton Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Na daɗe cikin sana'ar motoci sannan mafi yawa daga cikin motocin da jami'an tsaron suka ɗauko daga gidajena waɗanda na siyo ne daga Amurka da daɗewa tun kafin na zama gwamna."

Ya musanta cewa an kwaso motoci 40 a gidajensa

Da yake martani kan iƙirarin da jami'an tsaron suka yi na kwaso motoci 40 a gidanjensa, Matawalle ya ce tatsuniya ce kawai sannan ya ƙalubalance su da su nunawa duniya motocin ta gani.

"Jami'an tsaron kamata ya yi su nuna motocin 40 domin mutane su gani. Duk wanda ya san Matawalle ya san cewa na daɗe cikin sana'ar motoci tun kafin na zama gwamnan jihar Zamfara." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Ashsha: Matawalle Ya Bayyana Irin Satar Da Gwamnatin Zamfara Ta Yi Masa a Gida Da Sunan Kwacen Motoci

Matawalle ya kuma yi zargin cewa jami'an tsaron gaban kansu kawai suka yi suka kutsa masa cikin gidaje domin babu wanda ya sanar da shi.

Matawalle Ya Ce An Masa Sata a Gida

A wani labarin na daban kuma, tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya ce jami'an tsaro sun yi masa satar kayayyakin iyalansa lokacin da suka shiga gidajen.

Matawalle ya ce hijaban matansa sai da jami'an tsaron suka ɗauka lokacin da suka je kwaso motoci a gidan.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk wani abu mai muhimmanci bai tsira ba inda har lefen ƴaƴansa aka yi awon gaba da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng