Matawalle Ya Yi Martani Bayan Gwamnatin Zamfara Ta Kwashi Motoci a Gidansa

Matawalle Ya Yi Martani Bayan Gwamnatin Zamfara Ta Kwashi Motoci a Gidansa

  • Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya zargi gwamnatin jihar Zamfara da satar kayen iyalansa lokacin ƙwato motoci a gidansa
  • Bello Matawalle ya bayyana wannan aika-aikar a matsayin aikin talauci da tsabar sakarci daga wajen gwamnatin jihar
  • Matawalle ya ce an shigar masa gida bada izni ba kuma hijaban matansa da lefen ƴaƴansa da zai aurar aka tattara aka kwashe

Jihar Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ta Dauda Lawal Dare, sata taje yi a gidansa.

Hakan na zuwa bayan gwamnatin jihar tace ta ƙwato motoci masu yawa a gidan tsohon gwamnan waɗanda ya yi awon gaba da su bayan ya bar mulki.

Matawalle ya ce sata gwamnatin Zamfara ta yi masa a gida
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle
Asali: UGC

A ranar Juma'a ne jami'an tsaro suka shiga gidajen Matawalle guda biyu, a birnin Gusau da kuma Maradun, inda suka ƙwato motoci har 40.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara Ya Faɗi Babban Dalilin Kai Samame Gidan Matawalle, Ta Ce Ta Kwato Motoci 40

An yi masa sata a gida

Tsohon gwamnan a yayin hira da BBC Hausa, ya bayyana wannan matakin da gwamnatin ta ɗauki a matsayin sakarci da talauci ina har kayan matansa aka sace a gidajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matawalle ya bayyana cewa hatta hijaban matansa basu tsira ba daga wannan abin kunyar da gwamnatin jihar ta aikata masa.

A kalamansa:

"Dukkan ɗakunan matana babu wanda ba a shiga ba, har da hijabi na mata aka kwashe. Hatta irin murhun nan na garwashi, duka an saka cikin mota an tafi da su."
"Ɗakunan matana duk sun fasa, har da hijaban matana duk sun kwasa, sun kwashi turamai na iyalina, akwai lefen ƴaƴana da zan aurar gabaɗaya sun kwashe shi."

Matawalle ya ce ba a nemi izninsa ba kafin a shigar masa gidaje

Matawalle ya bayyana cewa ba a sanar da shi ba kafin a yi masa kutse zuwa cikin gidan nasa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Kujerar Ministan da Aka Masa Tayi Bayan Ganawa da Shugaba Tinubu

Tsohon ya bayyana cewa hassada ce kawai da baƙin ciki suka sanya aka shigar masa cikin gidaje aka kwashe motocin.

Matawalle ya bayyana cewa da yawa daga cikin motocin da aka kwashe a gidansa na Maradun, motoci ne waɗanda mutane suka ba shi gudunmawa lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya kuma ƙara da cewa wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya saye su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna saboda ya daɗe yana taɓa sana'ar siyar da motoci.

Mun Kwato Motoci Masu Tsada 40 a Gidan Matawalle, Gwamnatin Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da ƙwato tsadaddun motoci har guda 40 daga gidan tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Gwamnatin ta ƙwato motocin ne bayan ta tura jami'an tsaro zuwa gidajensa da ke a birnin Gusau da Maradum a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng