Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Emefiele

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Emefiele

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya daga kan kujerarsa
  • Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele daga mukaminsa a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni
  • Gwamnatin tarayya ta ce an dakatar da shi ne saboda binciken da ake gudanarwa a ofishinsa da kuma wasu gyare-gyare da ake yi

Labari da ke zuwa mana a yanzu haka ya kawo cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan labarai na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey ya fitar a yau Juma'a, 9 ga watan Yuni.

Asiwaju Bola Tinubu da Godwin Emefiele
Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dakatar Da Emefiele Hoto: @officialABAT and @cenbank
Asali: Facebook

Sanarwar ta ce:

"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, CFR, daga ofis nan take.

Kara karanta wannan

Godwin Emefiele: Shin Shugaban Kasa Bola Tinubu Na Da Ikon Dakatar Da Gwamnan CBN? Lauya Ya Yi Bayani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan ya biyo bayan binciken da ke gudana a ofishin sa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a ma'aikatar kudi na tattalin arziki.
"An umurci Mista Emefiele da ya gaggauta mika harkokin ofishinsa ga Mataimakin Gwamna (bangaren ayyuka), wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan babban bankin kasar har sai an kammala bincike da kuma gyara."

Daily Trust ta rahoto cewa tun a lokacin yakin neman zabensa, Tinubu ya bayyana cewa manufar sauya kudin kasar wanda ya haifar da karancin kudi a kasar wani yunkuri ne na kawo karan tsaye ga babban zaben kasar.

Sai dai kuma, Tinubu ya bugi kirjin cewa zai lashe babban zaben duk rintsi duk wuya.

Bayan lashe zaben nasa, ana ta rade-radin cewa Emefiele na iya rasa kujerarsa a karkashin gwamnati mai ci a yanzu.

Da na hadu da Kwankwaso a fadar Villa, da ina iya dauke shi da mari, Ganduje

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu da Kwankwaso Sun Shiga Ganawa a Fadar Shugaban Kasa

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa idan da ya hadu da magajinsa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar shugaban kasa da ke Abuja da ya mare shi.

Da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu kan lamarin tsaro a jihar Kano bayan aikin rusau da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Ganduje ya nuna rashin gamsuwa da lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng