An Shiga Damuwa, A Yayin Da Hukumar Kwastam Ke Shirin Hana Shigo Da Kayan Sawa Na Gwanjo Najeriya

An Shiga Damuwa, A Yayin Da Hukumar Kwastam Ke Shirin Hana Shigo Da Kayan Sawa Na Gwanjo Najeriya

  • Hukumar kwastam ta ƙasa, ta bayyana aniyarta ta hana shigowa da kayayyakin sawa na hannu, wadanda aka fi sani da kayan gwanjo
  • Hukumar ta bayyana cewa, kayan na gwanjo na da illa ga lafiyar ƙasa, sannan kuma wasu na yin amfani da damar wajen mayar da Najeriya juji
  • Sai dai sanarwar ta tayar da ƙura, inda mafiya yawa daga cikin 'yan Najeriya masu amfani da kafafen sada zumunta suka nuna ƙin amincewarsu da matakin

Hukumar Kwastam ta bayyana aniyar ta na sanya dokar hana siyar da kayan sawa na hannu da aka fi sani da gwanjo a Najeriya.

A wata hira da aka yi da shi a kwanakin baya, kakakin hukumar kwastam, Abdullahi Aliyu Maiwada, ya bayyana cewa sayar da tufafin na gwanjo na da illa ga kasa, kamar yadda muka samu daga Blueprint.

Kara karanta wannan

Iska Mai Ƙarfi Ta Yi Sanadin Rasa Rayyuka 2 Da Lalata Gidaje 20 a Jigawa

Hukumar Kwastam za ta hana siyar da kayan gwanjo
Hukumar Kwastam na yunkurin hana shigowa da kayan gwanjo. Hoto: Liberty TV
Asali: UGC

Kayan gwanjo na da illa ga lafiyar ƙasa, cewar jami'in kwastam

A cewar kakakin na hukumar kwastam:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Tufafin gwanjo na da illa ga lafiyar ƙasa, a saboda haka ne ma gwamnati ke ganin ya dace a haramta sayar da su.
“Ya kamata mutum ya yi tunani. Babu wanda ya san yadda ko kuma wanda ya yi amfani da waɗannan tufafin. Kuma babban abu ma, ’yan fasa ƙwauri na son mayar da Najeriya wajen zubar da tarkace. Ba za mu lamunci hakan ba.
“Allah ya albarkaci ƙasarmu da tarin ɗan adam, da kuma albarkatu masu ɗumbin yawa. Don me wani zai je ya kawo mana kayayyakin da aka yi amfani da su?”

Sanarwa ta haifar da zazzafan martani daga masu amfani da yanar gizo-gizo

Jaridar The Nation, ta tattaro yadda wasu yan Najeriya suka yi martani kan sanarwar da jami'in na hukumar kwastam ya yi, ga abinda wasu ke cewa:

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Daga Hawa Mulki, Gwamnan Arewa Ya Kori Ma'aikata Daga Aiki

tonia.gram_ ta ce:

“A bar talaka ya lumfasa mana. Kar ku shaƙe mu."

Babajideedges ya ce:

“Na tabbata wanda ya kawo maganar hana cin ganda abar ƙaunata, shi ne ya kawo wannan maganar ma. Kar ku damu yadda ba su yi nasara ba game da ganda, nan ma ba za suyi ba.
Marasa lissafi kawai, waɗanda ke biyan mafi ƙarancin albashin 30k amma suna nan suna ƙoƙarin nuna wata isar ƙwandara.
wahal da kai kawai”

Brandy_ish ya yi sharhi da:

“Wadannan mutanen ba su ma san halin da mutane ke ciki. Wannan shi ne yadda talakawa ke iya samun sutura. Ta ya ya aka albarkace mu da mutane marasa hankali a matsayin shugabanni? Indai ba gani suka yi mai kuɗi ya bai wa talaka tazara ba, hankalinsu ba zai kwanta ba. Allah ka ceci ƙasar nan, don ni ban ma gane komai yanzu."

Hukumar Kwastam ta yi babban kamu a Legas

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Dauki Zafi Bayan Gano Yaudarar da Aka Yi Wajen Shigo da Jirgin Nigeria Air

A farkon shekarar nan ta 2023, Legit.ng ta kawo muku wani rahoto kan wani gagarumin kamu da hukumar ta kwastam ta yi a jihar Legas.

Hukumar ta yi nasarar kama kayan sojoji, 'yan sanda, da ma wasu ƙwayoyi masu tarin yawa a filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammad da ke Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng