Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutun Dimokuradiyya

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutun Dimokuradiyya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun dimokuraɗiyya a faɗin ƙasar nan domin murnar zagayowar ranar
  • Gwamnatin tarayyar ta sanar da ranar Litinin 12 ga watan Yunin 2023, a matsayin ranar hutu saboda zagayowar ranar dimokuraɗiyya
  • Ana gudanar da bikin zagayowar ranar dimokuraɗiyya a Najeriya a kowace ranar 12 ga watan Yuni a faɗin ƙasar nan

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutu domin bikin ranar dimokuraɗiyya.

Jaridar The Nation tace babbar sakatariyar ministirin cikin gida Dr Oluwatoyin Akinlade, ita ce ta bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar hutun dimokuradiyya
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Babbar sakatariyar ta taya ƴan Najeriyaa murnar zagayowar wannan rana mai cike da ɗumbin tarihi.

Akinlade, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa dimokuraɗiyya a Najeriya ta ga faɗi tashi tun bayan ƙafuwarta, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Gwamnoni Sun Ziyarci Tinubu, Sun Bayyana Matsayarsu Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya ta taya ƴan Najeriya murna

A cikin sanarwar Akinlade ta bayyana cewa duk da faɗi tashin da aka samu a wajen kafuwar dimokuraɗiyya a ƙasar nan, har yanzu ƴan Najeriya basu sare guiwa ba wajen ganin tabbatuwarta.

"Duk da haka ƙasar, hukumominta da abu mafi muhimmanci al'ummar Najeriya sun tsaya kai da fata wajen ganin kafuwar mulkin dimokuraɗiyya." A cewarta.
"A wannan lokacin mai cike ɗumbin tarihi, ana kira ga ƴan Najeriya da ƙawayen ƙasar da su yaba da ci gaban da aka samu, su yi murna kan nasarorin da aka samu sannan su yi fatan samun dimokuraɗiyya mai kyau a ƙasar."

Tinubu Ya Umarci Shettima Ya Fito da Tsarin Taimakon Talaka

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana aniyarsa ta rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da ƴan Najeriyaa suka tsinci kansu a ciki a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Peter Obi Ya Bayyana Zabinsa a Kujerar Shugabancin Majalisa

Shugaban ƙasar ya umarci mataimakinsa, Kashim.Shettima, wanda shine shugaban majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC), da ya fito da tsare-tsaren da za a taimakawa talakawa saboda cire tallafin man fetur ɗin.

Majalisar za ta kuma yi duba kan yiwuwar ƙarin albashi ga ma'aikata duk domin rage raɗaɗin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel