Wasu Tsaffin Gwamnonin Arewa Sun Bada Gudunmawa Wajen Samun Karfin Yan Ta’adda, Uba Sani

Wasu Tsaffin Gwamnonin Arewa Sun Bada Gudunmawa Wajen Samun Karfin Yan Ta’adda, Uba Sani

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana yadda wasu tsofaffin gwamnonin arewa suka haddasa tabarbarewar tsaro a yankin
  • Malam Uba Sani ya ce ya san lokacin da wasu tsoffin gwamnonu suka rika zama wuri ɗaya da yan ta'adɗa, suna taimaka masu
  • A cewarsa, kafa 'yan sandan jihohi ne kaɗai mafita ga kalubalen tsaron da ake fama da su a ƙasar nan

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya zargi wasu tsoffin gwamnoni a Arewa maso Yamma da cin amanar ƙawancen da jihohi suka ƙulla don samar da tsaro.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Gwamnan na cewa tsoffin gwamnonin sun yi wa ƙawancen zagon ƙasa ta hanyar, "ɗasawa," tare da yan bindiga da 'yan ta'adda.

Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani: Yadda Wasu Gwamnoni Ke Cin Abinci Tare da Yan Ta'adda Hoto: Sen Uba Sani
Asali: Facebook

Uba Sani, wanda ya ƙi ambatar suna a zarginsa, ya yi ikirarin wasu gwamnoni sun ɗauki, "hanyar da ba zata ɓulle ba," wajen shawo kan rashin tsaro a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Labule Da Kungiyar Ma'aikata Ta Kasa Kan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

A cewarsa, ɗaukar irin waɗannan hanyoyin mara sa kyau ne suka jawo arewa ta wayi gari cikin ƙaƙanikayi da tabarbarewar tsaro mai muni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sani ya faɗi haka ne a wata hira da Channels tv cikin shirin Sunrise Daily ranar Talata, inda ya ƙara da cewa:

"Akwai lokacin da gwamnatin Kaduna da wasu jihohin Arewa Maso Yamma, harda jihar Neja mai iyaka da mu, suka haɗa kai domin lalubo hanyar magance matsalar tsaro."
"Mun haɗa kwamitin haɗin guiwa, asusun haɗin guiwa, muka rika aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro kamar hukumar sojin ƙasa, sojin sama da rundunar yan sanda."
"Abun takaici ana cikin haka, wannan ƙawance ya rushe lokacin da wasu gwamnoni suka zagaye suka tuntubi yan bindiga da yan ta'adda, su tattauna da su, kuma su basu kuɗaɗe."

Hanya ɗaya ce zata magance matsalar tsaro a ƙasar nan - Uba Sani

Kara karanta wannan

Jerin Manyan Malaman Addini Da Suka Kyale Malanta Suka Zama Gwamnoni a Jihohinsu

Gwamma Sani ya ƙara da cewa kirkirar yan sandan jihohi ne hanya ɗaya tilo da zata iya kawo karshen kalubalen tsaro a Najeriya.

Ya ce wannan ya zama kusan wajibi idan aka yi la'akari da ƙarancin karfin ikon gwamnoni a kan hukumomin tsaro.

Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro Kan Harin da Yan Bindiga Suka Kai

A wani labarin kuma Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya kira taron tsaro kan kazamin harin da yan bindiga suka kai ranar Asabar.

Gwamna Aliyu, wanda ya katse tafiyar da ya yi zuwa Abuja kan harin, ya lashi takobin hana 'yan bindiga da sauran yan ta'adda sakat a Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262