Wasu Makasa Sun Bindige Farfesan Jami'ar Ibadan Har Lahira

Wasu Makasa Sun Bindige Farfesan Jami'ar Ibadan Har Lahira

  • Wasu mahara ɗauke muggan makamai sun harbe Farfesan jami'ar Ibadan, a babban birnin jihar Oyo har lahira ranar Litinin da daddare
  • Abokin aikinsa ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce bayan kashe farfesa, makasan sun kuma yi awon gaba da motarsa
  • Hukumar makarantar ta tabbatar da kisan amma ta ce ba ta san su waye suka aikata ba kawo yanzu

Ibadan, Oyo - Wani Farfesa a fannin ilimin Social and Environmental Forestry na jami'ar Ibadan (UI) da ke jihar Oyo, ya rasa rayuwarsa a hannun wasu mahara da ake zaton makasa ne.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun bindige Farfesa Opeyemi Ajewole a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, yayin da yake hanyar komawa gida ranar Litinin da daddare.

Ajewole.
Wasu Makasa Sun Bindige Farfesan Jami'ar Ibadan Har Lahira Hoto: Opeyemi Ajewole
Asali: Facebook

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa lamarin ya faru da misalin karfe 9:00 na daren ranar Litinin, 5 ga watan Yuni, 2023 a kan babban titin Ojoo-Oyo.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Dauki Zafi Bayan Gano Yaudarar da Aka Yi Wajen Shigo da Jirgin Nigeria Air

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, wani abokin aikin mamacin ya ce makasan sun yi ajalin Ajewole yayin da yake kan hanyar komawa gida, kamar yadda Tribune online ta tattaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Dagaske ne, an kashe shi jiya da daddare yayin da ya kama hanyar koma wa gida. Maharan sun harbe shi har lahira kana suka yi awon gaba da motarsa. Abokina ne."

Hukumar jami'a ta tabbatar da aukuwar lamarin

Babban mataimakin Rijistara kuma jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar UI, Mista Joke Akinpelu, ya tabbatar da kisan malamin makarantar kuma Farfesa.

Ya bayyana cewa tabbas wasu mahara da ba'a san ko su waye ba sun yi ajalin Farfesa Ajewole amma ba su da tabbacin ko harin na fashi da makami ne ko wani abu daban.

A kalamansa, Mista Joke Akinpelu, ya ce:

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

"Eh dagaske ne lamarin ya faru, amma bamu da tabbacin ko maharan 'yan fashi da makami ne ko makasa ne da wasu suka ɗauki haya don aikata wannan ɗanyen aikin."

Wani dalibin jami'ar UI, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa labarin kisan Farfesa Ajewole, ya ɗaga musu hankali saboda mutum ne da bai da matsala.

Ya ce mutum ne mai fara'a da jawo ɗalibansa a jiki, kuma baya ƙyamar kowa domin har hannu yana bai wa ɗalibansa su gaisa.

A kalaman ɗalibin ya ce:

"Allah Sarki, rayuwa kenan, idan ka ga Farfesa Ajewole zaka sha mamaki, mutum ne mai fara'a, mai jawo ɗalibansa a jiki, ya zama tare da su ya basu hannu, kuma kullum yana cikin farin ciki."
"Na san shi sosai, ya taɓa rike shugaban tsangayar da nake karatu (HOD) a Jami'ar Ibadan. Ina rokon Allah ya tona asirin waɗanda suka aikata wannan kisan."

Kara karanta wannan

Tirkashi: ’Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ta Damfari Mutane Fiye da 100 Kudi Har N150m

Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro

A wani rahoton na daban kuma Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya kira taron tsaro kan kazamin harin da yan bindiga suka kai ranar Asabar.

Gwamna Aliyu, wanda ya katse tafiyar da ya yi zuwa Abuja kan harin, ya lashi takobin hana 'yan bindiga da sauran yan ta'adda sakat a Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262