Babu Batun Daukar Ma’aikata: Yadda Wani Mutum Ya Ci Abinci a Otal Din da Mutum-Mutumi Ke Cinikayya
- Wani bidiyon da aka yada a TikTok ya nuna wani gidan cin abinci da babu alamar mutum, sai dai mutum-mutumi
- Bidiyon ya nuna yadda wani mutum ya zo ya ba da odar abinci, mutum-mutumi ya dauko ya kawo masa kamar mutum
- Ba sabon abu bane ganin irin wadannan abubuwa a kasashen waje, musamman yadda fasahar zamani ke kara yaduwa
A wani bidiyon da aka yada, an gano wani gidan cin abinci da kwastomomi ke odar abinci ta hanyar sanar da mutum-mutumi ba dan Adam ba.
Bidiyon da @notkevinlasean ya yada a TikTok ya nuna yadda gidan cin abincin mai suna Robot Restaurant da ke birnin Tokyo a Japan ke harkallarsa.
Mutum-mutumi mai kawo abinci
Bidiyon ya fara ne yayin da wani mutum ya kira mai kawo abinci; wanda yake mutum-mutumi tare da ba da odar nau’in abincin da yake bukata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan bidiyon ya yanke zuwa wani wurin, inda aka nuna mutum-mutumin dauke da faranti cike da abinci ya nufi teburin da mutumin ke zaune.
Babu sauran ciwon kai
Shi kansa kwastoman, ya yi mamakin yadda mutum-mutumin ke aiki cikin tsanaki ba tare da samun wani tsaiko ba.
Bidiyon dai ya dauki hankalin mutane da yawa a kafar sada zumunta, inda suke bayyana ra’ayoyinsu ga wannan fasahar.
Wannan dai ba sabon abu bane a birnin Tokyo, domin akan yi yawan karo da shagunan siyar da abinci da sauran wurare da dama da ke amfani da mutum-mutumi.
Kalli bidiyon:
Martanin jama’a
@Potatocat:
“Kalli yadda su uku suke kallonka.”
@zee74848:
“Ya za a yi idan masifaffiya irin Karen ta shigo ta fara tsawa ga mutum-mutumi.”
@user4758588484:
“Dan uwa sai waka yake a cikin zuciyarsa.”
@Jullen:
“Yanzu kenan babu wanda zai samu sana’a.”
@egm657:
“Kamar wurin su Sam da Cat.”
@JODIO:
“Za ka iya duba kudaden haraji na, sh ne abin da ya bani dariya.”
@Marle:
“Ba zai yiwu ba, dan uwa ka bi a hankali.”
A wani lokaci baya, mun kawo maku rahoton yadda wani gidan cin abinci ke amfani da mutum-mutumi wajen kula da gidan abinci a wata kasa.
Asali: Legit.ng