Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu a Wani Kazamin Harin Yan Bindiga a Jihar Benue

Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu a Wani Kazamin Harin Yan Bindiga a Jihar Benue

  • Tsagerun yan bindiga sun kai kazamin hari wasu garuruwa a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue
  • Maharan sun kashe mutane masu yawan gaske sannan sun jikkata wasu da dama da ke kwance a asibiti a yanzu
  • Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an gano gawarwakin jama'a daga dazazzuka

Benue - A kalla mutane 13 ne aka kashe bayan wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai mummunan hari garuruwan jihar Benue.

Mazauna garin Imande Mbakange da sauran garuruwan da ke makwabtaka a yankin Mbacher na karamar hukumar Katsina-Ala sun yi zargin cewa wasu yan bindiga da ke addabar yankin ne suka aiwatar da harin.

Taswirar jihar Benue
Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu a Wani Kazamin Harin Yan Bindiga a Jihar Benue Hoto: Oasis Magazine
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa a cikin shekarun da suka gabata, jami'an tsaron hadin gwiwa a yankin sun dakile ayyukan miyagun da ake zargi da aikata fashi da makami, garkuwa da mutane da yawan harbin mutane a yankin a ranar kasuwa da lokacin jana'iza.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wasu 'Yan Daba Sun Farmaki Ayarin Gwamnan Arewa a Hanyar Dawowa Daga Abuja

Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala ya yi martani

Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Atera Alfred, ya fada ma jaridar a kan wayar tarho cewa harin ya faru ne lokaci guda a safiyar ranar Asabar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alfred ya tabbatar da gano gawarwakin mutane 13 zuwa yanzu daga dazuzzuka zuwa yammacin Asabar, yana mai cewa mutane da dama sun jikkata kuma suna jinya a asibitoci daban daban yanzu haka.

Hadimin labaran shugaban kasar hukumar, Tsar Tartor ya nakalto shi yana yin Allah wadai da lamarin wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da jikka wasu da kuma kona gidaje da dama na miliyoyin naira.

Shugaban kasarar hukumar ya bayyana kisan da yan bindigar suka yi a matsayin rashin imani da dabbanci yana mai kira ga dukkanin hukumomin tsaro da su ninka kokarinsu wajen magance sabbin hare-haren cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Gama Gari, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa’adi

Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin

Da aka tuntube shi, jami'ar hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa babu cikakken bayani zuwa yanzu, rahoton Nigerian Tribune.

An kama barawon waya da ya shari bacci a coci

A wani labari na daban, mun ji cewa wani sharararran barawon wayoyi ya shiga hannun rundunar yan sanda a jihar Osun.

Matashin ya tafi coci da niyan sace wayoyin masu bauta amma sai bacci ya dauke shi, bayan ya tashi sai ya kowa ya watse don haka ya mika hanyar gida, amma yan sanda suka cafke shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng