Tsohuwar Ministar Buhari Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Hukumar EFCC Ta Tasa Keyarta

Tsohuwar Ministar Buhari Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Hukumar EFCC Ta Tasa Keyarta

  • Tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta bayyana cewa ita ta kai kanta ofishin hukumar EFCC a Abuja ranar 2 ga watan Yuni
  • A cikin wata sanarwa, Tallen ta yi ƙarin haske kan cewa ba a kamata ba, kuma ita ce a ƙashin kanta ta je domin zargin ƙaryar da aka ƙaƙaba mata
  • Ana dai tuhumar tsohuwar ministar ta gwamnatin Buhari ne da laifin karkartar da makuɗan kuɗaɗe da suka kai N2bn

FCT, Abuja - Tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta yi magana kan binciken da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ke yi a kanta, kan zargin aikata laifin cin hanci, cewar rahoton The Cable.

Tsohuwar ministar ta hallara a ofishin hukumar na birnin tarayya Abuja, a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Tsagerun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutum 2 a Birnin Tarayya Abuja

Pauline Tallen ta yi magana kan tuhumar da EFCC ke yi mata
Pauline Tallen ta musanta EFCC ta cafke ta Hoto: Punch.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa Tallen ta amsa tambayoyi ne kan zargin karkatar da N2bn na shirin wanzar da zaman lafiya na matan shugabannin ƙasashen Afirika (AFLPM).

Da ta ke magana kan lamarin cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni, tsohuwar ministar ta bayyana cewa ita da ƙashin kanta ta je ofishin EFCC, kuma ba gayyatarta aka yi ba ko kama ta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tallen tace ta je ofishin hukumar ne domin yin magana ƙan zarge-zargen ƙarya da ake jifarta da su. Sai dai, ba ta yi cikakken bayani kan zarge-zargen ba.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Saboda girma da mutuncin tsohon shugabana, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ofishinsa, da farko ban yi magana kan zargin da ake min ba, amma yanzu ya zama dole na yi hakan."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: EFCC Ta Titsiye Tsohuwar Ministar Buhari Kan Karkatar Da Biliyan N2

"Da farko, matakin da ya fi dacewa da ace wannan bincike ne na gaskiya, kamata ya yi a tuntuɓi ministirin harkokin mata domin bincikar duk kuɗaɗen da aka turo mata."
"Amma kawai a yanke hukunci ba tare da bincike ba, ya nuna tsantsar rashin ƙwarewa wajen aiki, da shin mutunta ministirin harkokin mata, sannan ya taɓa ƙima da darajata."
"Haka kuma ina son na bayyana cewa babu wata gayyata a hukumance daga hukumar EFCC, sannan ba a tsare ni ba."

EFCC Ta Titsiye Tsohuwar Ministar Buhari Kan Karkatar Da N2bn

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta tsare tsohuwar ministar harkokin mata, a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Jami'an hukumar ta EFCC sun tsare Pauline Tallen ne bisa zargin karkatar da N2bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng