Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Basarake da Wasu Mutum 2 a Abuja
- Wasu miyagun yan bindiga sun shiga kauyen Abuja, sun sace basarake da wasu mutane 2 da tsakar daren Alhamis
- Bayanai daga mazauna garin da harin ya faru sun nuna cewa yan bindigan sun shafe sama da sa'a ɗaya suna cin karensu ba babbaka
- Hakimin Ketti, wanda ya tabbatar da aukuwar harin ya yi kira ga gwamnatin Tinubu ta tashi tsaye
Abuja - 'Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Ketti da ke yankin ƙaramar hukumar Abuja Municipal (AMAC), sun yi awon gaba da Dagacin ƙauyen, Mista Sunday Zakwoyi.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa bayan sace Basaraken, 'yan bindiga sun haɗa da wani ɗan gidan Sarauta, Mista Markus Gade, da wani mazauni mutum ɗaya.
Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa maharan akalla su 10 sun shiga garin ɗauke da manyan bindigu da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Alhamis.
A cewarsu, yan bindigan sun aikata ta'adi tun daga wannan lokaci har ƙarfe 12:50 na farkon awannin ranar Jumu'a, suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muna rokon gwamnati ta kawo mana agaji - Hakimi
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, hakimin Ketti, Mista Alex Akata, ya yi kira ga hukumomin tsaro su kai musu agaji domin har ta kai jallin da basu iya bacci.
Akata ya ƙara da cewa mako uku da suka shige masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da mutanen garin akalla su 3, daga ciki harda Ɗanladi Aliyu, wanda har yanzu yana hannunsu.
Bisa haka ya yi kira ga sabuwar gwamnati karkashin shugabancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ta ƙara zage dantse ta yi duk me yuwuwa wajen tabbatar da tsaro a birnin tarayya.
Basaraken ya koka kan cewa rashin kayan aiki ne babban abinda ke ƙara kawo tabarbarewar tsaro a yankinsu, kana ya buƙaci shugaban ƙaramar hukumar AMAC da mahukuntan Abuja su dube su.
Na Siyar da Jaririna Don Magance Matsalolin Iyali, Cewar Wata Mata a Yayin Da Ta Shiga Hannun Hukuma
Hakimin ya ce duk tsawom lokacin da maharan suka shafe suna aikata ta'adi a garin, babu jami'in tsaron da ya kawo musu ɗauki.
Shin yan bindigan sun nemi fansa?
Wani ɗan uwan daya daga cikin mutanen, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce sun tura kuɗin fansa ga masu garkuwan amma har yanzu shiru ba su sako ɗan uwansu ba.
Yan sanda sun daƙile harin yan ta'adda a Katsina
A wani labarin kuma Dakarun Yan sanda sun dakile hari, sun sheke yan bindiga 2 a jihar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Mai magana da yawun hukumar yan sanda a jihar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce dakarun sun halaka hatsabiban yan bindiga 2 a musayar wuta.
Asali: Legit.ng