Wike Ya Kare Tinubu Kan Cire Tallafin Mai, Ya Ce Ciyar Da Najeriya Gaba Sai An Tauna Tsakuwa

Wike Ya Kare Tinubu Kan Cire Tallafin Mai, Ya Ce Ciyar Da Najeriya Gaba Sai An Tauna Tsakuwa

  • Tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya magantu a kan cire tallafin mai da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi
  • Wike ya ce wannan mataki na Tinubu ya yi daidai domin sai an dauki tsauraran matakai idan har ana son kai kasar gaba
  • Jigon na PDP ya ce suna tare da sabon shugaban kasar don ya nuna lallai aikin ya zo yi da gaske

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya kare hukuncin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin man fetur, cewa ba abu mai sauki bane shugabantar kasar irin Najeriya.

Wike ya bayyana hakan ne a wani dan takaitaccen hira da manema labarai na fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni.

Wike da Tinubu
Wike Ya Kare Tinubu Kan Cire Tallafin Mai, Ya Ce Ciyar Da Najeriya Gaba Sai An Tauna Tsakuwa Hoto: Daily Post Nigeria
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa Wike da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da tsohon Gwamna James Ibori na jihar Delta sun gana da shugaban kasar a fadar shugaban kasa a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Babban Abokin Faɗan Tinubu Ya Ajiye Kayan Yaƙi, Ya Shirya Zai Karɓi Tayin Kujera

Da yake martani ga wata tambaya kan dalilin ziyarar nasu, Wike ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Babu wani babban abu game da shi, gwamnan na jihar Oyo ya fada maku abun da muka zo yi; basa goyon baya. Muna goyon bayan duk shawarwari da ya yanke, ya nuna cewa ya shirya ma aikin kuma babu abu game da hakan. yana bukatar daukar tsauraran matakai don kasa ta ci gaba."

Da aka tambaye shi ko yana shirin sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce:"Kada ku fadi haka."

Makinde ya magantu kan cire tallafin mai

Da farko, Gwamna Makinde ya ce sun ziyarci shugaban kasar ne don fada masa cewa ya fara aiki da kyau kuma yana da goyon bayan mutane baki daya.

Da aka tambaye shi game da lamarin tallafin mai, gwamnan na jihar Oyo ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Ba Hafsoshin Tsaro Sabon Salon Yaki da Rashin Tsaro a Najeriya

"Eh, mun tattauna shi. Abu ne da mutane ke tattauna shi sosai a yanzu. Mun san shawarace mai wahala ga mutane kuma yana bukatar goyon bayan kowa don wuce wannan yanayi."

Makinde da Wike sun kasance manyan gwamnonin G5 da suka kasance sahun gaba yayin da rikicin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi zafi gabannin zaben 2023.

Yan siyasar biyu sun taimaka wajen nasarar da shugaban kasa Tinubu ya samu a zaben na 25 ga watan Fabrairu.

Cire tallafin mai: Tinubu ya yi tsokaci kan duba mafi karancin albashi

A wani labarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya magantu a kan batun sake duba karancin albashin ma'aikatan Najeriya.

A cewar Tinubu, ya zama dole a sake bitar karancin albashin ma'aikatan domin ya yi daidai da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng