Dan Majalisar Adamawa Ya Koma Hawa Keke Saboda Tsadar Man Fetur

Dan Majalisar Adamawa Ya Koma Hawa Keke Saboda Tsadar Man Fetur

  • Kasar Najeriya ta rincabe yayin da mutane musamman talakawa suka shiga wani hali bayan sanar da cire tallafin man fetur
  • Dan majalisa kuma babban mai tsawatarwa a majalisar dokokin Adamawa, Hon. Haruna Jilantikiri, ya ajiye motarsa inda ya koma ga keke
  • Jilantikiri ya ce ya dauki matakin ne domin sajewa da talakawa da suka zabe su domin a cewarsa baya tunanin za su iya hawa motoci da wannan tsadar man fetur din

Adamawa - Babban mai tsawatarwa na majalisar dokokin jihar Adamawa, Hon. Haruna Jilantikiri, ya zabi komawa ga hawan keke domin yin zanga-zanga ga tashin farashin man fetur.

Dan majalisar, wanda ke wakiltan mazabar Madagali a majalisar jihar, ya ce ya yanke shawarar ajiye motarsa da amfani keke don gudanar da harkokinsa na yau da kullun, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Manajan NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Hon. Haruna Jilantikiri a kan keke
Dan Majalisar Adamawa Ya Koma Hawa Keke Saboda Tsadar Man Fetur Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Farashin man fetur ya kusa ninkawa sau uku bayan Shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana cewar zamanin tallafin man fetur ya kare.

Ba na tunanin jama'a za su iya hawa mota yanzu, Jilantikiri

Hon. Jilantikiri wanda ya zanta da manema labarai yayin da yake tuka kekensa, a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, ya koka game da farashin man fetur a yanzu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce baya tunanin cewa al'ummar kasar za su iya hawa motoci duba ga yanayin da tattalin arziki ke ciki a yanzu.

Hon. Jilantikiri ya koka:

"Ya kamata mu faka motocinmu sannan mu yi amfani da kekuna don sajewa da wadanda suka zabe mu don bana tunanin za su iya hawa mota ko tuka baburansu a yanzu."

Dan majalisar ya roki gwamnatin tarayya da ta gaggauta duba lamarin domin magance wahalar da talakawa ke sha.

Kara karanta wannan

Zanga-Zanga Kan Cire Tallafin Man Fetur: Kungiyar Kwadago Ta Fitar Da Muhimmiyar Sanarwa

Ba ma shirin yin kowace zanga-zanga ta gama gari, kungiyar NLC

A wani labarin, kungiyar kwadago ta kasa, ta karyata rade-radin da ke yawo cewa tana shirin gudanar da wata zanga-zanga ta gama gari a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni kan cire tallafin mai da hauhawan farashinsa.

NLC ta bayyana cewa sabanin haka, tana da wata ganawa da za ta yi domin tattauna lamarin a ranar Juma'an kuma cewa za ta sanar da jama'a matakin da ta dauka bayan taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng