Tsohon Kakakin Buhari Ya Samu Aiki Kwanaki Kadan Bayan Barin Mulki

Tsohon Kakakin Buhari Ya Samu Aiki Kwanaki Kadan Bayan Barin Mulki

  • Tsohon kakakin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya koma kan sabon aiki kwanaki kaɗan bayan karewar mulki
  • Femi Adesina, a wata hira ranar Talata, ya ce zai koma kamfanin jaridar TheSun karo na biyu a matsayin mataimakin shugaba
  • Gabanin Muhammadu Buhari ya naɗa shi mukami, Adesina ya rike matsayin shugaban narubutan TheSun

Tsohon mai bai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, shawara ta musamman kan midiya da yaɗa labarai, Femi Adesina, ya samu aiki kwanaki kaɗan bayan sauka daga mulki.

Daily Trust ta rahoto cewa tsohon kakakin Buhari zai fara aiki a matsayin mataimakin shugaban kamfanin jaridar Sun daga ranar 1 ga watan Satumba, 2023.

Femi Adesina.
Tsohon Kakakin Buhari Ya Samu Aiki Kwanaki Kadan Bayan Barin Mulki Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

Mista Adesina ya rike muƙamain shugaban marubutan jaridar TheSun kafin daga bisani tsohon shugaban ƙasa Buhari ya naɗa shi a matsayin mai magana da yawunsa.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Ƙasa Ya Shiga Ofis, Ya Faɗi Gaskiya Kan Batun Cire Tallafin Man Fetur

Jaridar Punch ta rahoto cewa Mista Adesina ne da kansa ya tabbatar da samun wannan aiki a wata hira da ya yi ranar Talata. Sanata Orji Kalu, mamallakin jaridar ne ya amince da naɗin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa ban bar TheSun ba

A cewar Adesina, bayan Buhari ya naɗa shi mukami, ya yi niyyar murabus daga aikin jaridar TheSun, amma Sanata Kalu ya ba shi shawarar kar ya yi kurkuren yin murabus.

Ya ce a wannan lokaci Kalu ya masa tayin dawowa kan aiki idan muƙamin gwamnatin bai masa ba ko kuma bayan sun gama mulki na tsawon shekaru Takawas.

A jawabinsa, Adesina ya ce:

"Ɗama na taso ne daga jaridar TheSun, a lokacin ina Manaja/shugaban Editocin jaridar kuma lokacin da na ce zan tafi, Dakta Orji Uzor Kalu ya ce kar na yi murabus, zaka iya shiga gwamnati ka ji baka son matsayin."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Rudani Yayin Da Rahoto Ya Yi Ikirarin Tinubu Ya Yi Nade-Naden Farko Bayan Rantsarwa

"Zamu yi maraba da kai a duk lokacin da ka dawo ko kuma kila ka shiga gwamnatin ku shafe shekaru Takwas, kana dawowa zamu karɓe ka, zan maida kai mataimakin shugaba."
"Ba wai maganar kawai ya faɗa mun ba har ya aiko mun da takardar sabon muƙamin, yanzu haka takardar ɗaukar aikin na nan a wurina."

Tinubu ya fara naɗa hadimai a gwamnatinsa

A wani labarin kuma Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun yi muhimman naɗe-naɗe guda 2 daga fara shiga Ofis ranar Talata.

Sabbim shugabannin sun karbi rantsuwar kama aiki daga wurin Alkalin alkalan Najeriya ranar Litinin a Filin Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262