Gyara Ilimi: Gwamna Zulum Ya Dumfaro, Zai Dauki Malamai 5,000 Aiki, Zai Kawo Sabon Tsarin Karantarwa
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya ce zai dauki malamai 5,000 don inganta harkar ilimi a jihar
- Gwamnan ya bayyana haka ne a bikin rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu a Maiduguri babban birnin jihar
- Ya ce makarantu a jihar za su fara karatun rana don rage cunkoso a dakunan karatu yayin da ake karatun safe
Jihar Borno – Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya ce gwamnatinsa ta yi alkawarin daukar malaman makaranta 5,000 don inganta ilimi a jihar.
Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da shi da aka yi a karo na biyu a Maiduguri babban birnin jihar a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Ya kara da cewa za a fara zuwa makarantu da rana musamman firamare da sakandire don rage yawan cunkoso da ake samu da safe, da kuma rage yawan yara wadanda ba sa zuwa makaranta.
A cewarsa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Duk da mun gina sabbin manyan makarantu da kuma kara girman wadanda muke da su da kusan azuzuwa 1,000, muna fama da matsalar cunkoso a dakunan karatu da kuma babbar matsalar yara wadanda ba sa zuwa makaranta duk da suna matakin shekaru na zuwa makaranta.
“Ina farin cikin sanar da cewa jihar Borno za ta fara karatun rana a firamare da sakandire, na zabi kwamitin da zai kawo tsarin da zamu yi na karatun rana.
"Kwamitin har ila yau zai kawo mana makarantun da zamu fara da su a cikin manyan makarantun da muke da su wadanda suke da wutar lantarki.”
Ma'aikata masu zaman banza za su koma koyarwa
Zulum ya bayyana cewa fara yin karatun rana na bukatar karin malamai, shi yasa ya umarci shugaban ma’aikatan da ya zakulo ma’aikatan da suke zaman banza a sakatariyar gwamnati don a musu bitar yadda za su iya koyarwa a makaranta musamman na zuwan rana.
Za'a dauki matakan tsaro don kare daliban rana
Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya ce za a dauki matakai masu tsauri na tsaro don tabbatar da samun nasara a karatun ranan, inda ya ce makarantar ranan na iya zarcewa har lokacin almuru.
A kokarin ganin an inganta harkar ilimi, Gwamna Zulum ya bayyana shirinsa na daukar malamai 5,000 a wa’adin mulkinsa da zai shiga.
Gwamna Zulum Zai Sake Gina Wasu Kauyuka 3, Buhari Ya Ba Da Gudumawar N15bn
A wani labarin, Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi alkawarin sake gina wasu kauyuka guda uku da 'yan ta'adda suka lalata.
A cewarsa, wannan aiki zai taimaka wajen dawo da mutanen da suka tarwatse da kuma 'yan gudun hijira dawo wa muhallinsu.
Asali: Legit.ng