Shugaban AIT, Raymond Dokpesi, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ranar Rantsarwa
- Mamallakin gidan talabijin ɗin AIT da kuma Raypower FM, Raymond Dokpesi, ya rasu ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023
- Marigayin, shugaban kamfanin Daar Communications kuma jigon jam'iyyar PDP ya cika ne bayan fama da jinya
- A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun ce zasu yi cikakken bayani kan shirin jana'iza nan gaba kaɗan
FCT Abuja - Shugaban kamfanin Daar Communications, Raymond Dokpesi, ya riga mu gidan gaskiya a birnin tarayya Abuja ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023.
A cewar rahoton da jaridar Punch ta tattaro, Marigayi Dokpesi, wanda babban jigo ne a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya rasu yana da shekara 71 a duniya.
An samu labarin rasuwar Mista Dokpesi, mamallakin gidan talabijin ɗin AIT da kuma Raypower FM, a wata sanarwa da iyalansa suka fitar ranar Litinin.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Sanarwan ka cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Cikin tsananin ƙunci da karayar zuciya muke sanar da rasuwar High Chief Raymond Aleogho Anthony Dokpesi (Ezomo na masarautar Weppa-Wanno) wanda Allah ya yi wa cikawa ranar 29 ga watan Mayu."
"Marigayi High Chief Dokpesi ya kasance Miji, Uba, Kaka da kuma abokin wasu wanda muke ƙauna da zuciyarmu. Duk wanda ya taɓa mu'amala da shi zai yi matuƙar kewarsa."
"Mutum ne da ake girmamawa kuma ɗan kasuwan da ya yi fice wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimaka wa al'umma. Ayyukan alherinsa ba zasu gushe ba."
"Iyalansa zasu sanar da cikakken bayanai kan rasuwarsa nan ba da jimawa ba haɗe da shirye-shiryen yi masa jana'iza. Muna fatan ransa ya samu salama," inji sanarwan.
Wata majiya ta ce mamacin ya mutu a Asibitin Abuja bayan ya gamu da bugun zuciya a lokacin da aka kammala watan Azumin Ramadan na wannan shekarar.
Tun wannan lokaci ya ke fama da jinya a Asibiti gabanin yau Allah ya masa cika wa.
Shugaba Tinubu Ya Ɗauki Mataki Mai Kyau Kan Sauya Takardun Naira
A wani labarin kuma Sabon Shugaban ƙasa ya ce zai yi nazari san tsariɓ sauya fasalin naira wanda tsohon shugaban ƙasa Buhari ya gudanar.
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai sake nazari kan tsarin Buhari na sauya fasalin N200, N500 da N1000. A cewarsa tsarin ya kuntatawa talakawa.
Asali: Legit.ng