An Yi Wa Sarkin Kano Ihu A Wurin Bikin Rantsar Da Abba Gida Gida, Bidiyo Ya Bayyana
- Dandazon magoya bayan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, mai kayan marmari sun yi wa Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ihu a filin wasa na Sani Abacha
- A filin wasan ne ake yin bikin kaddamar da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin sabon gwamnan jihar Kano
- Nan take, bayan sarkin mai sanda mai daraja ta daya ya iso wurin taron, magoya bayan jam'iyyar NNPP suka fara yi wa sarkin ihu cikin fushi
Jihar Kano - Gwamna mai barin gado, Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano zai mika mulkin jihar ga zababben gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu na 2023.
Yusuf, jigo ne na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP kuma na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar ta Kano, wanda shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da isar sarkin wurin taron, magoya bayan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party suka fara masa ihu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Kalli bidiyon zuwan sarkin wurin taron a nan.
A cewar rahotani, an yi wa mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, kanin Sarkin Kanon irin wannan ihun.
Amma jami'an tsaro sun yi gaggawa sun shiga tsakani sun raka sarakunan zuwa wurin zamansu.
"Zan bincike bashin N241bn", Sabon Gwamnan Kano ya aika sako da Ganduje
Tunda farko, Legit.ng ta rahoto cewa Yusuf ya sha alwashin bincikar bashin naira biliyan 241 da gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, gwamna mai barin gado ya bar masa.
A cewar Yusuf Kabir, takardun mika mulki da Abdullahi Ganduje ya mika masa ta hannun Sakataren Gwamnatin Jiha ba su wadatar ba.
Abin da yasa Yusuf na NNPP zai sake duba batun tsige Sanusi, Kwankwaso ya magantu
Kazalika, Legit.ng ta rahoto cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya bada tabbacin cewa gwamnatin ta Kano mai shigowa za ta bibiyi batun tsige Alhaji Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano na 14.
Batun yiwuwar dawo da Sanusi kan karagar mulki ya janyo muhawara a shafukan sada zumunta a kasar.
Asali: Legit.ng