Sai Na Kwace Mulkin Najeriya, Rantsar da Tinubu Zai Kara Min Karfin Gwiwa, Inji Peter Obi

Sai Na Kwace Mulkin Najeriya, Rantsar da Tinubu Zai Kara Min Karfin Gwiwa, Inji Peter Obi

  • Rantsar da Bola Ahmad Tinubu zai kara masa kwarin gwiwar cewa, tabbas zai kwace mulkin kasar nan ba tare da wata matsala ba
  • Ya fadi hakan ne yayin da ya saura sa'o'i kadan a rantsar da Tinubu kana ga batun da ke gaban kotu a yanzu
  • Ya zuw ayanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Tinubu, Peter Obi da hukumar zabe mai zaman kanta a kotu

Najeriya - Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, ya ce rantsar da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai kara masa karfin gwiwar neman kwace mulkin kasar nan.

Daily Trust ta rawaito cewa Tinubu ,wanda ya lashe zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, za a rantsar da shi a matsayin babban kwamanda kuma shugaban Tarayyar Najeriya na 16 a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Bankwana: Buhari ya ba Sadiya Farouq lambar yabo saboda yadda take tausayin 'yan Najeriya

Tuni shirye-shiryen taron rantsarwar ke ci gaba da wakana, inda jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da aikinsu yadda ya kamata.

Peter Obi ya magantu kan rantsar da Tinubu
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shirin rantsar da Tinubu ya kankama

Manyan baki da suka hada da tawagar shugaban kasar Amurka Joe Biden, sun isa babban birnin tarayya Abua domin halartar bikin mai muhimmanci ga 'yan Najeriya da ma duniya baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake amsa tambaya mai alaka da bikin rantsarwar a wani shafin Twitter, Obi ya ce ba zai ja da baya ba a yakin neman tabbatar da nasararsa a zaben da ya gudana a bana.

A cewarsa:

“Ban fara wannan gwagwarmayar a rana daya ba; Na san ba zai zama abu mai sauki ba. Bikin rantsarwar za ta ma kara min karfi ne.”

Peter Obi ya mika sako ga masoyansa

Channels Tv ta ruwaito cewa, da yake aika sako ga fusatattun mabiyansa da ke babatu da tofin Allah-tsine ga Tinubu a kafafen sada zumunta, Obi ya ce:

Kara karanta wannan

Ahaf: Bana son Tinubu, amma idan ya bani minista zan karba, fasto Bakare ya fadi dalili

“Ina rokonku ku tsaya cikin taitayinku. Wannan batu ne da ya shafi canji wanda ke daukar lokaci."

Amurka ta turo wakilai zuwa bikin rantsar da Tinubu

A bangare guda, gwamnatin kasar Amurka ta turo wakilanta don halartar bikin rantsar da Bola Ahmad Tinubu na Najeriya.

Gobe Litinin ne za a rantsar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin sabon shugaban kasan Najeriya na 16 a jere.

Ya zuwa yazu yanzu, masu ruwa da tsaki na ci gaba da shiri, kasar Amurka ma ba a barta a baya ba tunda ta aiko wakilai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.