Buhari Ya Yaba da Aikin Sadiya Umar Farouq, Ya Ba Ta Lambar Yabo Mai Girman Gaske
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba minista Sadiya Umar Farouq saboda tsananin aiki tukuru da ta yi a karkashin mulkin Buhari
- Rahoto ya bayyana cewa, shugaban ya yaba mata, inda ya bayyana nasarorin da aka samu daga ma’aikatar ta jin kai da walwala
- Baya wannan ne karon farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ba da lambobin yabo ga jami’an gwamnati ba
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari GCFR ya baiwa ministar jin kai da walwala Sadiya Umar Farouq lambar yabo ta CON, Vanguard ta ruwaito.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati ta fitar ranar Lahadi 28 ga Mayu, 2023.
Sadiya na daga cikin mutane 75 da suka samu lambar yabo ta kasa da gwamnatin ta bayar.
An ba ta lambar yabon CON ne bisa gudunmawa da kokarin da ta yi daga watan Agustan 2019 zuwa 28 ga Mayu, 2023 wajen ba da tallafi ga yakar talauci Korona da dai sauran ayyukan jin kai.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Buhari ya yabawa Sadiya bisa jajircewa da yiwa ‘yan kasa aiki
A tun farko, shugaban kasa Muhammadu ya bayyana irin ayyukan ministar na jin kai da walwalar jama’a a matsayin nasarorin da ya cimma a mulkinsa.
Buhari a jawabinsa ya ce gwamnatinsa ta yi kokari wajen yakar talauci da sauran lamurran da suka shafi al’umma a lokuta mabambanta a kasar.
Kafin nan, Buhari ya yaba tare da jinjinawa minista Sadiya bisa irin ayyukan da ta yi na jin kai a karkashin gwamnatinsa.
Sadiya ce ministar farko a ma’aikatar jin kai da walwalar al’umma, kuma tana daga ministocin da ke yawan jin cece-kuce da suka daga ‘yan Najeriya.
Buhari ya karrama Burutai da lambar yabon CFR
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki lambar yabo, inda ya ba tsohon hafsun sojin Najeriya, Tukur Yusuf Burutai.
Wannan na zuwa ne a watan Oktoban 2022, inda shugaban ya tara jama’a da dama a fannonin kasar nan daban-daban tare da ba su lambobin yabo.
A cewar gwamnati, Burutai ya cancanci wannan lambar yabo, kuma tabbas ya yi aiki tukuru don tabbatar da ci gaban Najeriya, musamman ta fuskar tsaro da yaki da ta’addanci.
Asali: Legit.ng