Dakarun Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'addan ISWAP a Jihar Borno
- Dakarun sojoji na rundunar ƙasa da ƙasa (MNJTF) sun samu nasarar tura wasu ƴan ta'addan ISWAP zuwa inda ba a dawowa
- Dakarun sojojin sun tura ƴan ta'addan zuwa barzahu a yayin wani sintiri da suka fita a wani yanki da ke iyaka da tafkin Chadi
- Wani daga cikin sojojin ya samu rauni a yayin artabun da sojojin suka yi da ƴan ta'addan, inda aka garzaya da shi asibiti domin ba shi kulawa
Jihar Borno - Dakarun sashi na uku na rundunar sojin tsaro ta ƙasa da ƙasa (MNJTF), sun halaka ƴan ta'addan ƙungiyar Islamic State of the West Africa Province (ISWAP) mutum uku a jihar Borno.
Zagazola Makama, wani majiya wanda ya mayar da hankali kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun baƙunci lahira ne a ranar Lahadi.
Tashin Hankali Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Sake Kai Mummunan Hari Kan 'Yan Sanda a Jihar Ebonyi, Sun Halaka Da Dama
Dakarun sojojin sun haɗu da ƴan ta'addan ne lokacin da su ke sintiri a tsakanin iyakar tafkin Chadi da Malam Fatori, cikin ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.
Wata majiyar sirri ta bayyana cewa ƴan ta'addan sun gamu da ajalinsu ne a hannun dakarun bataliya ta 86 ta rundunar MNJTF.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Dakarun sojojin sun ƙwato makamai a hannun ƴan ta'addan
Majiyar ta bayyana cewa, dakarun sojojin sun kwato bindigu guda biyu ƙirar AK-47 a hannun ƴan ta'addan, inda ta ƙara da cewa wani soja guda ɗaya ya samu rauni a yayin musayar wutar, cewar rahoton The Cable.
An kai jami'in sojan da ya samu rauni zuwa asibitin sojoji a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin duba lafiyarsa.
Yan Ta’addan ISWAP Sun Yiwa Dakarunsu da Sojojin Najeriya Suka Kashe Jana’iza
A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda dakarun sojoji suka halaka ƴan ta'addan ƙingiyar ISWAP da dama a jihar Borno, da ke a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ƴan ta'addaɓ na ƙungiyar ISWAP sun taru a waje ɗaya domin yi wa ƴan'uwan su waɗanda suka haɗu da ajalinsu a hannun dakarun sojoji, jana'iza. Adadin yawan ƴan ta'addan da suka baƙunci lahira ya kai 60.
Asali: Legit.ng