Buhari Ya Bayyana Kadarorinsa, Ya Ce Babu Wanda Zai Tsira a Mukarrabansa Bai Bayyana Nasa Ba

Buhari Ya Bayyana Kadarorinsa, Ya Ce Babu Wanda Zai Tsira a Mukarrabansa Bai Bayyana Nasa Ba

  • Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari umarci dukkan masu madafun iko da su bayyana kadarorinsu
  • Ya ce tun daga kan mataimakinsa har zuwa kasa babu wanda zai tsira daga bayyana kadarorinsa
  • Kakakin shugaban, Garba Shehu shi ya bayyana haka a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu a Abuja

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana bin doka na bayyana kadarorinsa kafin da kuma bayan ya shiga ofishinsa don inganta aiki da kuma tarbiya a aikin gwamnati.

Kakakin shugaban ne, Mallam Garba Shehu ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Juma’a, ya ce yin hakan zai taimaka wurin yin gaskiya da kuma yaki da cin hanci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kadarorinsa
Buhari Yayin Bayyana Kadarorinsa, Ya Ce Babu Wanda Zai Tsira a Mukarrabansa. Hoto: Punch
Asali: Facebook

Buhari ya umarci dukkan masu madafun iko da masu mukaman siyasa tun daga kan mataimakin shugaban kasa har kasa da su karbi takardun don cikewa da kuma dawo da shi kamar yadda ya yi, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Daga Wurin Taron Miƙa Mulki, Shugaba Buhari Ya Faɗi Jihar da Jirginsa Zai Fara Sauka Kafin Tafiya Daura

Buhari ya ce babu wanda zai tsira tunda shima ya yi

Da yake magana bayan karbar takardar cikawa daga shugaban hukumar ka’idar aiki da da’a, Farfesa Isah Muhammad a ranar Juma’a, Buhari ya ce babu wanda zai tsira daga bayyana kadarorinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Na saka hannu, na karba. Daga nan zan tambayi manajan bankin da nake aiki da shi a Kaduna ya nuna min yanayin shiga da fitar kudi a asusun banki na.
“Babu wanda zai tsira daga bayyana kadarorinsa. Ina so daga mataimakin shugaban kasa ya yi kasa kowa yabi wannan tsarin.”

Mista Mohammed ya bayyana goyon bayan da Buhari ya ba su a shekaru takwas

Mista Mohammed ya ce bin wannan doka da shugaban ya ke yi a shekaru takwas da kuma goyon baya da ya ke bai wa hukumar ya taimaka sun cimma 99% wurin bin doka daga sauran masu mukamai a gwamnati, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Wanke Doguwa Daga Zargin Kisan Kai

Ya kara da cewa goyon bayan shugaban kasan ya taimaka wa hukumar wurin mai da harkokinta na zamani da kuma binciken matsaloli don aiki yadda ya kamata.

Shugaba Buhari Da Bola Tinubu Sun Zaga Fadar Shugaban Kasa

A wani labarin, Shugaba Buhari ya zagaya da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a fadar shugaban kasa don nuna masa muhimman wurare.

Buhari wanda ya ke kirga kwanaki don mika mulki ya zagaya da Tinubu ne yayin da ake shiye-shiryen mika mulki a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.