Yanzu Yanzu: El-Rufai Ya Tsige Magatakardar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

Yanzu Yanzu: El-Rufai Ya Tsige Magatakardar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya tsaya kan maganar da ya yi cewa zai ci gaba da korar ma'aikatan da suka gaza har zuwa ranarsa ta karshe a ofis
  • A wata sanarwa da kakakinsa, Muyiwa Adekeye ya saki a baya-bayan nan, ya bayyana cewa gwamnan ya amince da korar magatakardar majalisar dokokin jihar
  • Haka kuma, El-Rufai ya amince da korar wasu sakatarorin din-din-din biyu da ritayan wata daya

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai ya amince da korar Bello Zubairu Idris, a matsayin magatakardar majalisar dokokin jihar Kaduna.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye ya yi, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Nasir El-Rufai
Yanzu Yanzu: El-Rufai Ya Tsige Magatakardar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya kuma amince da sallamar wasu manyan jami'an gwamnati guda biyu a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daga Ƙarshe, Jirgin Saman Najeriya Ya Sauka a Birnin Abuja, Bidiyo

Wadannan jami'an sune Yau Yunusa Tanko, sakataren din-din-din, da Francis Kozah, sakataren sakataren hukumar bunkasa kasuwanci ta Kaduna (KADEDA).

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adekeye ya kuma bayyana cewa gwamnan ya amince da ritayar Stephen Joseph, wata sakatariyar din-din-din a jihar.

Wannan ci gaban na zuwa ne jim kadan bayan gwamnan ya ce a shirye yake ya yi gyare-gyare awanni 11 kafin barinsa kujerar mulki.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a makon jiya yayin da ya bayyana a wani taro inda ya yi magana kan shugabanci nagari, da kuma bukatar sanya mutane sama da komai a matsayin shugaba.

Gwamnan ya ce:

"Duk wani abu mara kyau da muka gano, za mu cire shi don gwamna na gaba baya bukatar sake yin haka.
"Ku yi ta zuba ido har zuwa awanni goma sha daya lokacin da zan bar mulki. Za mu ci gaba da korar bara gurbi da cire gurbatattun abubuwa."

Kara karanta wannan

Malami Ya Bayyana Gaban Kwamitin Majalisa Kan Ɓacewar Dala Biliyan 2.4 Na Ɗanyen Mai

El -Rufai ya tsige sarakuna 2 da hakimai 3 a Kaduna

A wani labarin, mun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya tsige Sarakuna biyu daga kan kujarer sarauta mako daya gabanin karewar wa'adin mulkinsa.

El-Rufai ya tsige rawanin Sarkin Piriga, Mai martaba Jonathan Paragua Zamuna, da kuma basaraken masarautar Arak, mai martaba Aliyu Iliyah Yammah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng