Kotun Koli Ta Aike Ta Gargadi Mai Tsauri Ga EFCC Da Wasu, Ta Bada Dalili
- Kotun koli ta gargadi Hukumar EFCC kan cin zarafin mukarraban gwamnatin jihar Kogi har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci
- Hukumar ta ce duk wadanda abin ya shafa da su guji daukar wani mataki har sai lokacin da babbar kotun ta yanke hukunci
- Yayin sauraran karar, Atoni na jihar Kogi ya zargi Hukumar EFCC da sauran hukumomin yaki da cin hanci da cin zarafi
FCT, Abuja – Kotun Koli a Najeriya ta gargadi Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da sauran hukumomi masu dakile cin hanci da kada su kuskura su sake cin zarafin wani mai mukamin gwamnati a jihar Kogi.
Hukumar ta ce dole su jira har sai ta yanke hukunci na karshe akan lamarin wanda Atoni Janar na jihar ya shigar, cewar Legit.ng.
TheCable ta tattaro cewa Atoni Janar din ya shigar da karar ne don kalubalantar dokar da ta samar da hukumomin yaki da cin hanci da kuma kasancewarsu a jihar.
Atoni na gwamnatin jihar ya yi zargin cewa ana cin zarafinsu
Yayin sauraran karar a ranar Talata 23 ga watan Mayu, lauya kuma Atoni na gwamantin jihar Kogi, Abdulwahab Muhammad ya yi zargin cewa ana cin zarafin mukarraban gwamnatin jihar a kotuna daban-daban.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kara da cewa da akwai kararraki a kotuna da ba a gama ba wadanda aka shigar tun a watan Faburairu ta shekarar 2023.
Lauyan Atoni na gwamnatin tarayya, T.A Gazali ya tabbatar wa kotun kolin cewa har yanzu bai samu bayanai na farko ba.
Hukuncin mai shari'a Amina Augie da 'yan kwamitinta
Mai shari’a, Amina Augie da kwamitinta mai dauke da mutane 7 na kotun kolin sun tunatarwa hukumar EFCC da sauran hukumomin cewa idan korafi na gaban kotu, dole mutane da hukumomi su jira har sai lokacin da kotu za ta yanke hukunci na karshe.
DSS Ta Bankado Kulla-Kullan Da Wasu Ke Yi Gabannin Rantsar Da Shugaban Kasa Da Gwamnoni a Fadin Najeriya
A karshe kotun ta bukaci dukkan wadanda abin ya shafa da kada su dau wani mataki har sai kotun ta yanke hukunci.
An dage ci gaba da sauraran karar har zuwa 10 ga watan Oktoba na wannan shekara.
Jami'in EFCC Ya Rasa Ransa Yayin Fada Da Abokan Aikinsa a Sokoto
A wani labarin, jami'in hukumar EFCC ya rasa ransa bayan fada da ya barke tsakaninsa da abokin aikinsa a Sokoto.
Jami'an mai suna Sufeto Abel Isah Dickson ya gamu da ajalinsa ne kan ajiyar wasu kaya da suka hada da kudi da magani.
Asali: Legit.ng