Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Sace Shahararren Malamin Addini a Adamawa
- Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani shahararren malamin addini, Rabaran Mike Ochigbo a jihar Adamawa
- 'Yan bindiga sun yi garkuwa da fitaccen mai wa'azin na gidan talbijin a ranar Laraba, 24 ga watan Mayu a gidansa da ke Nyibango
- Maharan sun kuma sace wani fasto mai suna John Moses duk a jihar ta arewa
Adamawa - Jaridar Punch ta rahoto cewa 'Yan bindiga sun yi garkuwa da shahararren mai wa'azin nan na gidan talbijin, Rabaran Mike Ochigbo a jihar Adamawa.
'Yan bindigar sun tisa keyar Ochigbo, wanda ya kasance shugaban cocin Freedom Power Chapel a safiyar Laraba, 24 ga watan Mayu daga gidansa da ke yankin Nyibango.
Hakazalika, an tattaro cewa mahara sun yi awon gaba da wani Fasto John Moses a wannan daren.
Wani mazaunin yankin, Joseph Kuna, wanda ya nemi a sakaya shi, ya ce, ya samu labarin cewa yan bindigar sun farmaki gidan babban faston da misalin karfe 2:00 na tsakar dare sannan suka yi awon gaba da shi bayan sun yi ta harbi a iska.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Joseph, ya samu labarin sace malamin addinin ne a safiyar yau.
Rundunar yan sanda ta yi martani
Kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje, ya ce an tura jami'ai yankin domin aikin ceto wadanda aka sace.
A cewarsa, kwamishinan yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, ya tura jami'an runduna ta musamman na SRRT da sauransu domin gudanar da aiki na musamman kan mabuyar miyagun tare da ceto Rabaran Mike Ochigbo da wani Fasto John Moses, wadanda yan bindigar suka sace.
Har yanzu ba a san inda babban malamin addinin yake ba. Wadanda suka yi garkuwa da shin basu tuntubi iyalinsa ba, rahoton sahara Reporters.
Rundunar yan sanda ta cika hannu da masu laifi a jihar Nasarawa
A wani labari na daban, mun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da kama wasu mutane 26 da ake zargi da aikata laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da kuma ayyukan asiri a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ne bayyana hakan a Lafia babban birnin jihar.
Asali: Legit.ng