Jerin Ministocin Buhari 14 Da Aka Fi Damawa Da Su A Gwamnatin Tarayya Daga 2015 Zuwa Yanzu
- Yanzu ana makon karshe na gwamnatin Muhammadu Buhari, za a samu canjin gwamnati a Najeriya
- Daga cikin Ministoci masu barin-gado akwai wadanda sun shafe kusan shekaru takwas da aka yi a ofis
- Irinsu Rotimi Amaechi da Ogbonnaya Onu sun ajiye aikinsu a 2022, suka nemi takarar shugaban kasa
A rahoton nan, Legit.ng Hausa ta tattaro Ministocin da tun a 2015 ake damawa da su a Gwamnatin Tarayya.
1. Zainab Shamsuna Ahmed
Da farko an nada Zainab Shamsuna Ahmed ne a matsayin karamar Minista, bayan Kemi Adeosun tayi murabus sai ta zama babbar Ministar kudi da tattalin arziki.
2. Mohammed Musa Bello
Tun da aka nada Ministoci a 2015, Malam Mohammed Musa Bello ya zama Ministan birnin tarayya Abuja, a 2019 ne ya samu karamar Minista a ma’aikatarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
3. Abubakar Malami
Abubakar Malami SAN ya shafe shekaru takwas ya na wakiltar jihar Kebbi a majalisar FEC a matsayin Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasa.
4. Babatunde Raji Fashola
A duk shekarun nan da aka yi, Babatunde Raji Fashola ne Ministan ayyuka da gidaje na kasa. A wa’adin farko shi ne ya ke kula da ma’aikatar wuta a Najeriya.
5. Rotimi Amaechi
Kafin ya yi murabus domin shiga takara, Rotimi Amaechi ya kasance a gwamnati tun da Muhammad Buhari ya rantsar da Ministocinsa a shekarar farko.
6. Chris Ngige
Chris Ngige ya yi kusan shekaru takwas a kujerar Ministan kwadago da samar da ayyukan yi. Tsohon Gwamnan ya yi niyyar yin murabus a bara, amma ya fasa.
7. Adamu Adamu
Daga cikin Ministocin da ba a canza ba akwai na harkar ilmi, Malam Adamu Adamu. Tun kafin samun mukamin, mutumin Bauchi ya na cikin na kusa da shugaban kasa.
8. Mustapha Baba Shehuri
Wani Minista da watakila ake yawan mantawa da shi a gwamnatin nan shi ne Mustapha Baba Shehuri, ya rike karamin Ministan wutar lantarki da Ministan gona.
9. Ogbonnaya Onu
Da Dr. Ogbonnaya Onu aka kafa gwamnatin nan, zuwa lokacin da ya yi murabus domin shiga takara, ya zama wanda ya fi kowa dadewa a ma’aikatar kimiyya.
10. Osagie Ehanire
A lokacin da Muhammadu Buhari ya nada Ministocin farko, Osagie Ehanire ya zama karamin Ministan lafiya, bayan an dawo karo na biyu sai ya zama babban Minista.
11. Geoffrey Onyeama
A tsawon mulkin nan, Geoffrey Onyeama ne Ministan harkokin kasar waje. Canjin da aka samu kawai shi ne canza mataimakinsa; Khadijah Bukar Abba da Zubairu Dada.
12. Suleiman Adamu
Injiniya Suleiman Adamu Husseini ya yi kusan shekaru takwas ya na rike da kujerar Ministan harkokin ruwa a gwamnatin Muhammadu Buhari, shi ya wakilci Jigawa.
13. Hadi Sirika
Kamar Ministan lafiya, Hadi Sirika ya samu karin matsayi a Agustan 2019 inda aka maida ma’aikatarsa ta jiragen sama ta balle daga karkashin ma’aikatar sufuri.
14. Lai Mohammed
Tsohon sakataren yada labaran APC, Lai Mohammed ne Ministan labarai da al’adu tun 2015, ya na cikin wadanda aka fi damawa da su a gwamnati mai barin-gado.
Asali: Legit.ng