CBN Ya Kara Kudin Ruwa Zuwa Kashi 18 'Don Dakile Hauhawan Farashin Kaya'
- Babban bankin Najeriya, CBN ta kara kudin ruwa zuwa kashi 18.5 bisa dari don dakile farashin kaya
- Gwamnan babban bankin Najeriya shi ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja
- An tabbatar cewa wannan ba shi ne karon farko da bankin ke kara kudin ruwan ba a kasar
FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya kara kudin ruwa zuwa kashi 18.5 cikin dari don dakile hauhawan farashin kayayyaki.
A makon da ya gabata, tashin farashin kayayyaki a kasar ya haura zuwa kashi 22.22 musamman hauhawan farashin kayan abinci.
Shugaban babban banki, Godwin Emefiele ne ya tabbatar da haka a ranar Laraba 24 ga watan Mayu ga manema labarai a sakatariyar bankin da ke Abuja.
Wannan ba shi ne karon farko ba da aka kara kudin ruwan
Wannan shi ne karo na uku da babban bankin ke kara kudin ruka a wannan shekara, cewar TheCable.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Emefiele ya ce mambobin kwamiti ne suka yanke shawarar kara kudin ruwan da kashi 18.5.
Ya kara da cewa kwamitin sun zabi barin CRR din da kashi 32.5 da kuma kudin ruwan da kashi 30, cewar Premium Times.
A cewarsa:
“Wannan farashi na yanzu babban bankin zai ci gaba da sa ido a kansa tare da hadin gwiwar sauran hukumomi na kudade saboda sarrafa yadda hauhawan farashin kayan ke tafiya".
Ya kara da cewa duk da hauhawan farashin kayayyakin masarufi ya zamo babban kalubale ga tattalin arzikin Najeriya, sauran bangarorin na tattalin arziki suna tafiya akan hanyar da ta dace duk da matsalolin.
A watan Janairu na wannan shekara, kwamitin ya kara kudin ruwan daga kashi 16.5 zuwa 17.5 saboda dakile matsalar hauhawan farashin kaya da kuma matsin lamba akan naira.
Matsalolin da 'yan Najeriya suka fuskanta
Duba da yadda ‘yan Najeriya suka fiskanci matsaloli musamman akan karancin naira, farashin kayan ya karu daga 21.91 cikin dari a watan Faburairu idan aka kwatanta da kashi 21.82 a watan Janairu.
Emefiele ya kara bayyana dalilin kara kudin ruwan
A ranar Talata, Godwin Emefiele ya bayyana cewa tsare-tsare masu tsauri na babban bankin an kirkiro su ne don shawo kan matsalolin tashin farashin kayan masarufi.
Emefiele Ya Shiga Tasku, Gwamnan Arewa Ya Bai Buhari Shawara
A wani labarin, Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci Buhari da kada ya biyewa dadin bakin Godwin Emefiele.
Gwamnan ya ce kada shugaba Buhari ya bar shugaban bankin CBN na fita karo karatu makwanni kadan kafin rantsar da sabuwar gwamnatin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng