Shugaba Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Gwamnatinsa Ta Gina Jami'ar Sufuri a Mahaifarsa Daura

Shugaba Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Gwamnatinsa Ta Gina Jami'ar Sufuri a Mahaifarsa Daura

  • Shugaba Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta gina jami'ar sufuri ta Daura ne don samar da isassun masu ilimin fasahohi da za su taimakawa harkokin sufuri
  • Ya bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da kamfanin Kajola na jihar Ogun, wanda zai riƙa ƙera taragon jiragen ƙasa
  • Shugaba Buhari ya kuma ce kamfanin na Kajola ne zai riƙa ƙera mafi akasarin taragon jiragen ƙasa da ake buƙata a yanzu

Legas - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta yi aiki tuƙuru wajen ganin ta buɗe jami’ar sufuri ta farko a garin Daura da ke jihar Katsina.

Ya bayyana cewa burin jami’ar shi ne samar da isassun ɗaliban da suka kammala karatun digiri, masu harkokin fasaha, ɓangaren sana’o'i, masu bincike a fannonin daban-daban na sufuri, musamman ma sufurin jiragen ƙasa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Ɗalibin Jami'a a Najeriya Ya Faɗi Ya Mutu Ana Tsaka da Wasan Kwallo

Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da ɗorewar ababen more rayuwa da gwamnatinsa ta zo da su kan harkokin sufurin jiragen na kasa.

Shugaba Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Gwamnatinsa Ta Gina Jami'ar Sufuri a Mahaifarsa Daura
Shugaba Buhari Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Gwamnatinsa Ta Gina Jami'ar Sufuri a Mahaifarsa Daura. Hoto: This Day
Asali: UGC

Kamfanin Kajola zai riƙa samar da tarago 500 a shekara

Ya yi wannan jawabi ne a Legas, a yayin ƙaddamar da kamfanin Kajola na Jihar Ogun, wanda shi ne irinsa na farko a Afirka ta Yamma da zai riƙa samar da taragon jirgi 500 a duk shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buharin, wanda ministan sufuri, Honarabul Muazu Sambo, ya wakilta ya ce:

“Saboda haka muna sa ran nan ba da jimawa ba ɗaliban da suka kammala karatu a Jami’ar Sufuri ta Daura, da waɗanda suka dawo daga jami’o’i daban-daban na kasar Sin waɗanda Messrs CCECC ta tura karatu, za su zo don maye gurabensu a ma'aikatar Kajola."

Tun 2019 aka sanya tushen ginin ma'aikatar

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ne ya ƙaddamar da harsashin ginin kamfanin a watan Nuwamban 2019 domin bunƙasa amfani da abubuwan gida a wajen zamanantar da layin dogon.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa, aikin wani shiri ne na wani kamfanin gine-gine da ƙere-ƙere na ƙasar Sin CCECC, wanda zai taimaka a aikin kilomita 157 da ake yi tsakanin Legas zuwa Ibadan.

A cewar Buhari, daga cikin tarago 368 da ake buƙata a yanzu da aka baiwa Messrs CCECC, za a kera kusan guda 220 a tashar Kajola kafin lokacin da za a mayar da ita zuwa babbar masana'antar kera taragai.

Aikin za taimakawa harkar sufurin jiragen kasa

A wani rahoto na jaridar The Guardian, mataimakin manajan daraktan kamfanin na CCECC, Jacques Liao, ya ce ma'aikatar za ta taimaka sosai wajen inganta ayyukan layin dogo a Najeriya.

Haka nan ya kara da cewa, aikin da kwamfanin zai rika gudanarwa zai samawa mutane da dama ayyukan yi.

Saura kwana 6 Buhari ya sauka, 'yar gidan shugaba Buhari ta yi magana

Hanan Buhari, 'yar gidan shugaba Muhammadu Buhari ta yi magana kan mahaifinta kwanaki shida gabanin ya bar mulki.

An dai jiyo hanan Buhari na jinjinawa shugaban kan kokarin da ya yi a wajen gudanar da mulkin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng