Minista Ya Cigaba da Korar Shugabannin Hukumomi, Ya Ce Babu Sani ko Sabo a Mulki

Minista Ya Cigaba da Korar Shugabannin Hukumomi, Ya Ce Babu Sani ko Sabo a Mulki

  • Matthew Pwajok ya rasa kujerar da yake kai ta shugaban hukumar NAMA, an kore shi daga ofis
  • Hadi Sirika ya maye gurbin shi da Tayib Adetunji Odunowo wanda yanzu haka Darekta ne a NCAA
  • A ‘yan kwanakin nan ne Ministan ya tsige Kyaftin Rabiu Yadudu daga FAAN, ya nada sabon Shugaba

Abuja - Korar manyan jami’an gwamnati da ake yi a ma’aikatar kula da harkokin jiragen sama bai kare ba, an sallami shugaban hukumar kasa ta NAMA.

A makon nan Daily Trust ta kawo rahoto cewa Matthew Pwajok ya rasa kujerarsa, sannan aka zabi Tayib Adetunji Odunowo a matsayin sabon shugaba.

Minista kula da harkokin jiragen sama, Hadi Sirika ya amince Tayib Odunowo ya canji Pwajok.

Minista
Ministan jiragen sama, Hadi Sirika Hoto: @nimetnigeria
Asali: Twitter

Hakan na zuwa ne bayan Sanata Sirika ya canza shugaban hukumar FAAN da ke kula da filayen jirgi, ya nada Kabir Yusuf Muhammed a makon jiya.

Kara karanta wannan

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya ke bayani da ya kaddamar da gyaran da aka soma yi wa filin tashin jirgi na Murtala Muhammed (MMA), Ministan ya tabbatar da haka a Legas.

Babu wata makarkashiya?

Ministan mai barin-gado ya fadawa manema labarai cewa Muhammadu Buhari ya amince da canje-canjen, kuma ya ce bai da wata muguwar manufa.

An rahoto Ministan ya ce Mai girma shugaban Najeriya ya yi abubuwan yabawa a mulkinsa a bangaren harkokin jirgin sama, ya ce ba za a manta da shi ba.

Gwamnati ba aikin kwana daya ba ne, shugabannin hukumomi su na da wa’adinsu, su na da lokacin da suke zuwa da lokacin da suke tafiya.

Babu wata boyayyar manufar. Shugabanci ne. Shugabancin mutum miliyan 250 ba wasa ba ne.

A rahoton da aka samu a The Nation, Ministan ya nuna ana korar shugabannin hukumomi da ma’aikatun tarayyar ne domin a kawo cigaba a fannin.

Kara karanta wannan

To fah: Saura kwana 8 Buhari ya sauka, ya kori babban daraktan FAAN, ya nada sabo

Tsohon ‘dan majalisar ya ce za a cigaba da korar shugabanni har zuwa ranar 29 ga watan Mayu.

Babatun Philip Agbese

A makon jiya, Shugaban kasa ya raba mukamai fiye da 10, hakan ya fusata wani Jagora a APC, kamar yadda aka samu labari, ya bukaci ayi bincike.

Philip Agbese ya bukaci Bola Tinubu ya yi bincike a kan mukaman karshe da aka bada, alal misali Toyin Madein da ta zama sabuwar AGF a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng