29 Ga Watan Mayu: Tambuwal Ya Yi Sabbin Nade-Nade Masu Muhimmanci
- Gabannin saukarsa daga mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya sanar da sabbin nade-nade
- Tsohon kakakin majalisar wakilan ya amince da nadin shugaban hukumar lafiya ta jihar da manyan jami'an makarantun gaba da sakandare
- An sanar da duk nade-naden ne a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu kuma sun fara aiki daga ranar Juma'a, 19 ga watan Mayu
Sokoto - Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya amince da nadin manyan jami'an makarantun gaba da sakandare na jihar da kuma babban sakataren hukumar kula da lafiya ta jihar.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa gwamnan ya bayar da sanarwar ne a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu wanda ga dukkan alamu shine nade-nade na karshe da zai yi kafin barinsa gidan gwamnati a mako mai zuwa.
A cewar sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, an nada Ibrahim Malami a matsayin shugaban hukumar lafiya ta jihar.
An tabbatar da cewar nadin nasa ya fara aiki ne a ranar Juma'a, 19 ga watan Mayu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar ta ce:
"An yi nadin ne bisa la'akari da tarin kokari, gogewa, kwazo da jajircewar babban likitan wajen yi wa jihar hidima.
"Gwamnan yana kira ga wanda aka nadan da ya kalli nadin nasa a matsayin kira na yi wa mutanen jihar Sokoto masu karamci hidima sannan ya yi masa addu'an samun jagorancin Allah wajen aiwatar da sabon aikin nasa."
Tambuwal ya nada manyan jami'an makarantun gaba da sakandare
A matakin makarantun gaba da sakandare, Gwamna Tambuwal ya kuma amince da nadin wasu manyan jami'an kwalejin ilimi na Sultan Ibrahim Dasuki, makarantar kimiyya da fasaha ta jihar.
Sai kwalejin kimiyya na Aisha Ahmad Gandi da kuma Kwalejin Musulunci na Haliru Binji.
A halin da ake ciki, bayan barinsa kujerar gwamna a mako mai zuwa, Gwamna Tambuwal zai ci gaba da kasancewa a harkar siyasa a matsayin dan majalisar tarayya a majalisar dattawa ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Mayu.
Gwamnatin Edo ta sallami malaman jami'a 13
A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta sallami lakcarori 13 na jami'ar Ambrose Alli (AAU) da ke Ekpoma.
An dai sallami ma'aikatan jami'ar ne bayan samunsu da hannu wajen aikata laifuka mabanbanta da suka hada da zamba, rashawa, lalata da sauransu.
Asali: Legit.ng