NNPC Ta Ci Gaba Da Aikin Tono Mai a Borno Bayan Shekaru 6 Da Dakatarwa

NNPC Ta Ci Gaba Da Aikin Tono Mai a Borno Bayan Shekaru 6 Da Dakatarwa

  • Kamfanin mai na NNPC a Najeriya zai ci gaba da bincike da kuma hakar mai a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas
  • Kamfanin ya bayyana yadda ya tsayar da aikin saboda matsalolin tsaro da suka addabi jihar a shekarun baya
  • Sannan kamfanin ya sanar da cewa aikin na karkashin kulawar wani bangare ne na kamfanin, NUPRC

Jihar Borno - Kamfanin mai na Najeriya (NNPC) ta ci gaba da bincike da hakar mai a Tafkin Chadi da ke jihar Borno.

Kamfanin ta bayyyana yadda ta tsayar da hakar mai din a shekarar 2017.

Ana tsammanin shugaba Buhari zai halarci bikin kaddamar da hakar mai din a gundumar Tuba da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno.

Tafkin Chadi a jihar Borno
Tafkin Chadi a jihar Borno. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A cewar shugabannin kamfanin, aikin na karkashin kulawar wani sashe na kamfanin mai ta kasa, NUPRC, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Sa Hannu, Ya Kawo Dokoki 8 a Makon Karshensa a Ofis

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An dade da fara hakar mai a jihar Borno

A rahoton, an tabbatar da cewa aikin binciken mai din an fara shi ne tun a shekarar 1976 zuwa har shekarar 1996 wanda ya kai aka tona kilomita 33,000 da ya kunshi yankin Gubio da Maiduguri da kuma Baga.

A ciki akwai rijiyoyi biyu (Wadi-1 da Kinasar-1) da aka samu gas wadda ba na kasuwanci a cikinsu, cewar The Guardian.

Tsakanin shekarar 2008 zuwa 2018, kamfanin mai ta Najeriya ta tona akalla kilomita kusan miliyan 2, yayin da a shekarar 2014 ta dakatar da hakar saboda rashin tsaro.

Kamfanin mai ta Najeriya a watan Juli na shekarar 2017 ta bayyana cewa an kai rabi a hakan mai din kafin rashin tsaro ya ta’azzara wadda ya yi sanadiyar kai hari kan ma’aikatan.

Bayan samun ingantaccen tsaro an ci gaba da aikin

Kara karanta wannan

“Allah Ya Amsa Addu’arta”: Yar Najeriya Ta Samu Miji Tana Da Shekaru 53, Ta Yi Wuff Da Angonta Mazaunin Turai a Bidiyo

Bayan tabbatar da ingancin tsaro a yankin, an ci gaba da aikin hakar a shekarar 2022 a rijiyar Wadi-B.

Da yake bayyana yadda aikin yake, Babban Daraktan kula da wannan sashe, Mukhtar Zanna ya ce kamfanin NNPC zai tono akalla kafa 14,000 a cikin rijiyar Wadi-B don neman mai da kuma abinda ke da alaka da gas.

“Muna da tabbaci saboda mun yi amfani da bayanai da muka samu, muna da sabon fasaha, munyi amfani da fasahar da muke da ita wurin sanin makaman aiki da kuma dabaru.

A nashi bayanin, Babban Darakta a sashin tonon mai ta kamfanin NNPC, Aminu Maitama ya ce suna da tabbacin samun mai a wurin.

“Mun yi imani da wannan wuri, muna da tabbacin samun mai anan kuma za mu samu mai da kuma gas da yakai yadda za a siyar.”

Buhari Ya Fadawa Kamfanin NNPC Ya Rage Farashin Fetur a Najeriya

A wani labarin, kamfanin mai na kasa, NNPC ta tafka asara yayin siyar da man fetus saboda nauyinsa.

Karamin ministan mai a kasar, Timipre Sylva ya bayyana halin da kamfanin ya tsinci kansa a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.