Shugaba Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Amince Ya Mayar Wa Borno Naira Biliyan 16

Shugaba Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Amince Ya Mayar Wa Borno Naira Biliyan 16

  • Shugaban ƙasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya buƙaci majalisar dattawa ta amince masa ya maida wa gwamnatin Borno N16bn
  • Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da Buhari ya aike majalisar kuma Sanata Ahmad Lawan ya karanta yau Talata
  • Buhari ya ce kuɗin na wasu titunan gwamnatin tarayya ne da gwamnatin Borno ta sa lalitarta ta gudanar

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya roƙi majalisar dattawan Najeriya ta sahale masa ya maida wa jihar Borno zunzurutun kuɗi naira biliyan N16bn.

The Nation ta tattaro cewa, Buhari, wanda zangon mulkinsa zai kare nan da kwana 6, yana neman maida wa gwamnatin Borno wannan kuɗin ne ta hanyar wani tsari, "issuance of promissory notes."

Shugaba Buhari.
Shugaba Buhari Ya Nemi Majalisa Ta Amince Ya Maida Wa Borno Biliyan N16bn Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ne ya karanta takardan bukatar shugaban ƙasan a zauren majalisa ranar Talata 23 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa Da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa

Muhammadu Buhari ya ce kuɗin da zai maida wa Borno sun ƙunshi na gina titunan gwamnatin tarayya wanda gwamnatin Borno ta aiwatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya kaddamar da rijiyar mai a Borno

A wani ɓangaren mai alaƙa da wannan, shugaba Muhammadu Buhari, ya kaddamar da fara haƙon ɗanyen mai a rijiyar Wadi-B a jihar Borno ranar Talata 23 ga watan Mayu.

Rijiyar Man Wadi-B da ke yankin ƙaramar hukumar Jere a jihar Borno, tana da nisan kilomita 50 daga Maiduguri, babban birnin jihar a Arewa maso Gabashin Najeriya.

A cewar kamfanin man fetur na tarayyan Najeriya (NNPCL), rijiyar man na da zurfin Ƙafa 14,000.

Kamfanin ya ƙara da cewa masu ilimin binciken ƙasa sun hango albarkatu masu ɗumbin yawa a wurin, kuma a ɓangarensa NNPCL zai yi duk yuwuwa don tabbatar da ɗanyen mai ne a wurin ko Gas ko kuma duka biyun.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Na APC Ya Sallami Kwamishinoni da Hadimai Daga Aiki, Ya Basu Lokaci Su Bar Ofis

Kotun Zaɓe Ta Amince da Muhimmiyar Buƙatar Atiku Kan Nasarar Tinubu

A wani rahoton na daban kuma kun ji cewa Kotun zabe ta amincu wa Atiku ya gabatar da shaidunsa cikin makonni 3 kamar yadda ya buƙata a baya.

Kotun ta baiwa Atiku tsawon mako uku ya gabatar da shaidu 100, waɗanda a cewarsa zasu gamsar da ikirarinsa cewa ba Tinubu ne ya ci zaben shugaban ƙasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262