Dangote Ya Bayyana Abin Da Buhari Ya Fada Masa Lokacin Da Ya Yi Niyyar Watsar Da Aikin Matatar Mansa

Dangote Ya Bayyana Abin Da Buhari Ya Fada Masa Lokacin Da Ya Yi Niyyar Watsar Da Aikin Matatar Mansa

  • Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana yadda Buhari ya kara mishi kwarin guiwa akan matatar mai ta Lagos
  • Dangote yace a cikin shekaru takwas na shugaba Buhari ya samu kwarin guiwar ci gaba da ginin matatar
  • Ya ce akwai lokacin da ya fara tunanin watsar da harkan man fetur, Buhari ne ya ci gaba da ba shi kwarin guiwa

Jihar Lagos - Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana yadda shugaba Buhari ya hana shi fasa ginin matatar man fetur da ke Lagos.

Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Latinin 22 ga watan Mayu yayin kaddamar da matatar inda ya ce kwarin guiwar da Buhari ya rinka bashi a cikin shekaru takwas, su suka kara masa kaimi wajen ganin ya assasa wannan matatar.

Dangote da Buhari a Lagos
Dangote da Buhari a jihar Lagos. Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lokacin da Dangote ya fara sha’awan shiga harkan man fetur ya kai shekaru 20 da suka wuce amma akwai matsaloli da dama da ya fiskanta.

Kara karanta wannan

Dangote Ya Zo Jihar Lagos Shekaru 45 da Suka Wuce Ba Shi da Komai, Cewar Gwamna Sanwo-Olu

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mai girma shugaban kasa da sauran baki, wannan tafiya ta kasance mai tsayi kuma mai cike da kalubale, hakan bai samu ba sai da goyon baya da kuma kwarin guiwan wasu daga cikin mutane.
“Zan fara da mai girma shugaban kasa, kwarin guiwar da ka yi ta bani a cikin shekaru takwas da suka gabata su ne silar kara min karfi wurin tabbatar da wannan matatar, a lokacin da na yi niyyar watsar da wannan al’amari kalmominka masu cike da tabbacin samun nasara sun sauya min tunani, mai girma shugaban kasa, nagode maka har cikin raina.”

Dangote ya godewa gwamnatin jihar Lagos

Dangote har ila yau ya godewa gwamnatin jihar Lagos tun daga farkon mulkin Bola Tinubu har zuwa wannan gwamnati mai ci ta Babajide Sanw-Olu, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Buhari Ya Sauka a Jihar Lagos Don Kaddamar da Matatar Mai Ta Dangote

Ya kara da cewa:

“Tun farkon lokacin mulkin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a wannan jihar da ya kirkiri matattarar kasuwanci ta Lekki, gwamna mai ci Babajide Sanwo-Olu ya kasance a cikin shiri kullum don tabbatar da wannan aiki, gwamnatin jihar Lagos tabbas ta bamu dama da goyon baya don ganin wannan aiki ya tabbata inda kamfanin mu ta zuba fiye da $30bn a tsawon wannan lokaci.”

Dangote Ya Zo Jihar Lagos Shekaru 45 da Suka Wuce Ba Shi da Komai, Cewar Sanwo-Olu

A wani labarin, Gwamna Sanwo-Olu na jihar Lagos ya yabawa Aliko Dangote kan kaddamar da matatar mai a jihar.

Gwamnan ya ce Dangote ya zo jihar ba shi da komai shekaru 45 da suka wuce amma ya kaddamar da irin wannan ma'aikata a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.