'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 18 a Wani Mummunan Hari a Jihar Benue

'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 18 a Wani Mummunan Hari a Jihar Benue

  • Ƴan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Benue, inda suka salwantar da rayukan mutum 18
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Iye da ke makwabtaka da jami'ar JOSTUM, cikin ƙaramar hukumar Guma
  • Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya auku da ranar Lahaɗi da misalin ƙarfe 7 na yamma

Jihar Benue - Aƙalla mutum 18 ne ƴan bindiga suka halaka a ƙauyen Iye na ƙaramar hukumar Guma a jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na yamma.

Mazauna garin sun kuma bayyana cewa mutane da dama sun samu munanan raunika a harin da aka kai a ƙauyen wanda ya ke kusa da jami'ar, Joseph Sarwuaan Tarka University Makurdi (JOSTUM).

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma Da Dama a Wani Mummunan Hari a Jihar Kaduna

'Yan bindiga sun halaka mutum 18 a jihar Benue
Rayukan mutum 18 suka salwanta a harin Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Wani mazaunin garin wanda ya rasa ɗan'uwansa a harin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun shigo ƙauyen da misalin ƙarfe 6 yamma lokacin da ake tsaka da cin kasuwar ƙauyen, cewar rahoton Vanguard.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

Ƴan bindiga sun kawo hari a ƙauyen Iye da misalin ƙarfe 6 na yamma ranar Lahadi. Sun halaka mutum 18 ciki har da ɗan'uwana. Harin ya auku ne ranar kasuwar Iye, lokacin da mutane su ke ta hada-hada.
"Harin abin takaici ne saboda an koro mu daga ƙauyen mu na Tse-Orvihi, cikin Uvir a ƙaramar hukumar Guma, inda mu ka samu mafaka a Iye, ga shi yanzu kuma sun zo sun halaka ɗan'uwana jiya."

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Christopher Waku, mai bayar da shawara kan lamuran tsaro na ƙaramar hukumar Guma, ya bayyana cewa mutum 18 ne suka halaka a harin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mutane Da Dama Sun Kone Kurmus a Wani Mummunan Hatsarin Mota Kan Titin Hanyar Lokoja-Abuja

A kalamansa:

“Jiya (Lahadi) an halaka mutum 18 a ƙauyen Iye cikin ƙaramar hukumar Guma, da misalin ƙarfe 6 zuwa 7 na yamma. Ƙauyen yana bayan jami'ar JOSTUM."

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar lamarin ta wayar tarho.

Sai dai, Anene ta bayyana cewa gawarwakin mutum bakwai kawai aka samo, yayin da aka samu gawa ɗaya ta cikin maharan.

'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma Da Dama a Kaduna

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun halaka wasu manoma da dama suna cikin aiki a gonakinsu a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun farmaki manoman ne a Unguwar Danko cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel