Sabuwar Matatar Man Dangote Zata Samar da Ayyuka Ga Yan Najeriya
- Sabuwar matatar man Ɗangote zata ɗauki ma'aikata 'yan Najeriya adadin ɗaruruwan dubbanni
- Shugaban kamfanin Ɗangote Group, Aliku Ɗangote ne ya bayyana haka a wurin kaddamar da matatar ranar Litinin a Legas
- Fitaccen ɗan kasuwan ya gode wa shugaba Buhari, Bola Tinubu da wasu gwamnonin Legas bisa goyon bayan da suka ba shi
Lagos - Shugaban kamfanin Ɗangote Group, Aliko Ɗangote, ya ce sabuwar matatan man Fetur ɗin da ya gina zata samar da, "ɗumbin ayyukan yi," ga matasan Najeriya.
Channels tv ta rahoto cewa Ɗangote ya bayyana haka ne ranar Litinin a Legas, a wurin bikin kaddamar da matatar man mai suna, "Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals."
Shugaban Najeriya mai barin gado, Muhammadu Buhari, ne ya jagoranci buɗe matatar man fetur ɗin, wacce ake sa ran zata samar da isasshen mai ga Najeriya.
Haka zalika ana tsammanin Matatar Ɗangote zata riƙa aikin samar da Man Fetur, Man Dizel, Man jiragen sama, kalanzir da sauran makamantansu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Adadin ma'aikata nawa matatar zata ɗauka aiki?
A kalamansa, Aliko Ɗangote ya ce:
"Wannan matatar mai zata samar da ɗumbin ayyukan yi ga 'yan Najeriya a cikin adadin da zamu kira dubbannin ɗaruruwa."
"Haka nan matatar zata samar da isasshen muhimman kayan aiki ga Masana'antun haɗa magunguna, abinci, kayan sha, gine-gine da sauran ma'ana'antu a ƙasar nan."
Ɗangote ya yaba da goyon bayan da ya samu
Fitaccen ɗan kasuwan ya bayyana godiyarsa bisa ɗumbin goyon bayan da ya samu a karan kansa da kuma kamfaninsa Dangote Group yayin gina wannan matata.
Ya yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da sauran 'yan Najeriya bisa goyon baya mara misaltuwa da suka nuna masa tun daga kafa tubalin ginin har zuwa yau da aka kammala.
Bugu da ƙari, ya gode wa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da baki ɗaya gwamnonin jihar Legas tun daga 1999, musamman gwamna mai ci Babajide Sanwo-Olu.
Gaskiya ta bayyana kam ganawar Tinubu da Kwankwaso
A wani labarin na daban, An bayyana babban dalilin ganawar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, da Rabiu Kwankwaso.
Zababben ɗan majalisar tarayya, Abdulmumini Jibirin, ya ce Tinubu ba mutum bane mai manta halacci, ba zai juya wa waɗanda suka taimakesa baya ba.
Asali: Legit.ng