Dangote Ya Zo Jihar Lagos Shekaru 45 da Suka Wuce Ba Shi da Komai, Cewar Gwamna Sanwo-Olu

Dangote Ya Zo Jihar Lagos Shekaru 45 da Suka Wuce Ba Shi da Komai, Cewar Gwamna Sanwo-Olu

  • Gwamna Babjide Sanwo-Olu ya yabawa Aliko Dangote saboda samar da katafaren kamfani a jihar Lagos
  • Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a babban taron kaddamar da matatar mai ta Aliko Dangote a jihar
  • Gwamnan ya ce shekaru 45 da baya Dangote ba shi da komai, amma yanzu ya sanya Afirka alfahari

Jihar Lagos - Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya yabawa shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote bisa kirkirar matatar mai a Najeriya musamman jihar Lagos.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin da yake Magana a bikin kaddamar da matatar a ranar Litinin 22 ga watan Mayu.

Matatar Dangote
Matatar Dangote da ke jihar Lagos. Hoto: Punch
Asali: UGC

Yace Dangote ya zo jihar Lagos daga Kano shekaru 45 da suka wuce ba shi da komai, amma yanzu ya samar da abubuwan da za su sanya Nahiyar Afrika alfahari, cewar jaridar Punch.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Buhari Ya Sauka a Jihar Lagos Don Kaddamar da Matatar Mai Ta Dangote

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Labari na farko shine na wani matashi dan Najeriya shekaru 45 da suka wuce, wanda ya zo jihar Lagos daga wani babban birni, Kano babu komai amma ya duba bambance-bambancen da muke da shi ya gina shahararren kamfani mai girma ga Afirka.”

Matatar Dangote wanda ta na karkashin babban kamfanin Dangote da ke samar da kayan masarufi daban-daban an kaddamar da ita yau a jihar Lagos.

Kamfanin wadda ya ke Ibeju-Lekki zai samar da danyen mai zuwa Nahiyoyi da dama da suka hada da Afirka da Asia da kuma Amurka.

Kamfanin zai samar da litan mai miliyan 38

Sannan zai samar da litan mai miliyan 38 na man fetus da bakin mai da kalanzir da kuma man jiragen sama ga Najeriya a kullum, cewar jaridar Daily Trust.

Matatar har ila yau za ta samar da ganga 650,000 na danyen mai wanda za a sarrafa shi zuwa bakin mai da gas da kalanzir da kuma mai da jiragen sama suke amfani da shi.

Kara karanta wannan

Matatar Man Dangote: Dalilin Da Ya Sa Muka Shiga Harkar Mai, Dangote Ya Yi Bayani

Buhari Ya Sauka a Jihar Lagos Don Kaddamar da Matatar Mai Ta Dangote

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a jihar Lagos don kaddamar da matatar mai Aliko Dangote.

Matatar da ke Ibeju-Lekki a jihar za ta fitar da litan man fetur miliyan 38 da kuma bakin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.