Ana Saura Kwanaki Kadan Ya Sauka, Buhari Ya Kori Babban Daraktan FAAN, Ya Nada Sabo
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi daidai lokacin da wa’adinsa na mulki ke cika a cikin wannan watan
- An nada sabon babban daraktan FAAN bayan cikar wa’adin tsohon daraktan kamar yadda rahotanni suka bayyana
- Rahoton da muka samo ya bayyana kadan daga gogewar aikin da sabon babban daraktan na FAAN yake dashi a aikin gwamnati
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da nada manajan tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, Kabir Mohammed a matsayin sabon babban daraktan hukumar zirganiyar jiragen sama ta FAAN.
Ana kyautata zaton zai fara aiki ne a ranar Litinin 22 ga watan Mayun nan, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Wannan nadi nasa na zuwa ne yayin da wa’adin tsohon babban daraktan na FAN, Kyaftin Rabiu Yadudu ya kare a kujerar.
Waye sabon babban daraktan FAAN kuma meye gogewarsa na aiki?
Kafin nada shi, Mohammed ya kuma kasance babban manajan yankin Arewa ta Tsakiya a hukumar ta FAAN.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An nada shi a matsayin shugaban tsara yadda harkokin jiragen sama za su kasance ta Aviation Implementaion Committee a watan Janairun 2022, rahoton Daily Sun.
Ministan harkokin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika ne ya ba shi wannan mukamai guda biyu a hadi, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Nadi kafin Buhari ya sauka da kwanaki takwas
Wannan nadi na gwamnatin Najeriya na zuwa ne yayin da ya saura kwanaki kadan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a mulki a cikin wannan watan na Mayu.
Idan baku manta ba, Buhari zai mika mulki ga Bola Ahmad Tinubu ne a ranar 29 ga watan Mayu, inda zai huta bayan shafe shekaru takwas sukutum yana jan ragamar Najeriya.
Akwai kura, ‘yan jam’iyyun adawa za su gabatar da shaidu a gaban kotu
A wani rahotonmu na baya, kunji yadda kotun raba gardamar zabe za ta saurari shaidu daga tsagin ‘yan jam’iyyun adawa a shari’ar da ake ta kalubalantar nasarar Bola Ahmad Tinubu.
Atiku zai kawo shaidu 100 gaban kotu, inda Peter Obi na jam’iyyar Labour yace shi dai shaidu 50 yake dasu da zai gabatarwa alkalai.
A bangaren INEC, APC da Tinubu, su ma sun bayyana adadin shaidun da za su gabatar cikin kwanaki kadan masu zuwa daidai da umarnin kotu.
Asali: Legit.ng