Da Dumi-Dumi: Wani Abin Fashewa Ya Fashe a Sokoto, Mutum Hudu Sun Halaka
- Wani abin fashewa da ya fashe a jihar Sokoto ya janyo asarar rayukan mutum huɗu, yayin da wasu da dama suka jikkata
- Lamarin dai ya auku ne a shagon wani mai walda a cikin ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto a Arewacin Najeriya
- Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ƙara da cewa mutanen da suka jikkata ana ba su kulawa a asibiti
Jihar Sokoto - Aƙalla mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata, bayan wani abin fashewa ya fashe a shagon wani mai walda a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi da rana.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ransa ya firgita lokacin ya ji ƙarar fashewar abin, inda ya yi tunanin cewa ƴan bindiga ne suka kawo hari a garin.
A kalamansa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Lokacin da na ji ƙarar fashewar, na yi zaton cewa ƴan bindiga ne suka kawo farmaki."
"Sai a lokacin da na ga mutane sun ruga da gudu zuwa wajen shagon mai waldar inda lamarin ya auku sannan hankali na ya kwanta cewa ba ƴan bindiga ba ne suka kawo hari."
"Bayan na yi bincike, an gaya min cewa fashewar ta auku ne a shagon wani mai walda, sannan an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama suka raunata.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ya tabbatar da cewa lamarin ya auku ne ranar Lahadi da rana.
Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana adadin waɗanda suka rasa ransu a matsayin mutum huɗu.
A kalamansa:
"Fashewar ba ta da alaƙa da rashin tsaron da yankin ya ke fama da shi. Ta auku ne a dalilin fashewar tulun gas a shagon wani mai walda a yankin wanda ya janyo asarar rayukan mutum huɗu.
"Waɗanda suka samu raunika suna cikin mawuyacin hali, sannan ana kula da lafiyarsu a wani asibiti wanda ba a bayyana sunansa ba a yankin."
Wani Bam Ya Tashi a Wata Mashaya a Birnin Jalingo Na Jihar Taraba
A baya rahoto ya zo kan yadda wani abun fashewa da ake kyautata zaton bam ne ya fashe a birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Abin fashewar dai ya fashe ne a wata mashaya da ke a cikin tsakiyar birnin, inda mutane da dama suka samu raunika.
Asali: Legit.ng