Yan Bindiga Sun Sheke Wani Manomi Saboda Ya Hana Dabbobinsu Shiga Gona a Jihar Arewa
- Wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan wasu manoma da suka yi kokarin hana dabbobinsu shiga gonaki a jihar Plateau
- Harin ya afku a ranar Lahadi 21 ga watan Mayu da safe a kauyen Kwi da ke karamar hukumar Riyom a cikin jihar
- Shugaban matasan kauyen Kwi, Solomon Dalyop ya ce maharan sun kashe wani matashi mai suna Nuhu Nyango
Jihar Plateau - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu manoma tare da hallaka daya daga cikinsu a kauyen Kwi da ke karamar hukumar Riyom a cikin jihar Plateau.
Harin wanda ya afku a ranar Lahadi 21 ga watan Mayu da safe ana zargin makiyaya da kai harin, a dai-dai lokacin da yankuna da dama ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Shugaban matasa na kauyen Kwi, Solomon Dalyop ya tabbatar wa jaridar Punch a birnin Jos cewa makiyayan sun kashe wani matashi mai suna Nuhu Nyango saboda ya hana dabbobinsu shiga cikin gonakinsu.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'an Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa, Sun Aiko da Sako Mai Ta Da Hankali
Shugaban matasan ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Abin da ya faru shi ne wasu manoma a kauyen Kwi a ranar Lahadi sun yi kokarin hana makiyaya shiga gonakinsu, amma ba su sani ba manoman na fake suna kallonsu a cikin daji.
“Da suka ga manoman na kokarin kora musu shanunsu daga wurin, sai makiyayan suka bude musu wuta tare da kashe daya daga cikinsu mai suna Nuhu Nyango, mun taru anan yanzu don mu binne shi.”
Rundunar 'yan sanda ba ta ce komai ba akan harin
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred bai ce komai ba dangane da harin saboda wayoyin hannunsa duka a kashe suke har lokacin tattara wannan rahoto, cewar jaridar The Times.
Shugabannin Kiristoci sun yi Allah wadai
A wata sanarwa da shugabannin Kiristoci a jihar suka fitar, sun yi Allah wadai da wannan harin inda suka kirayi hukumomi da su dauki tsauraran matakai don kawo karshen wadannan hare-haren.
A sanarwar da shugaban kungiyar, Rabaran Dr Stephen Baba Panya ya sanya wa hannu ya ce:
“Muna alhini da kuma bakin ciki yadda yanzu hare-haren ‘yan bindiga ya kara kamari musamman akan Kiristoci a kananan hukumomin Mangu da Riyom dake jihar Plateau.
“Hare-haren sun fara ne a Mangu a ranar Litinin 15 ga watan Mayu wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyin jama’a tare da batan wasu wandanda har yanzu ba a san inda suke ba."
Sanarwar ta kara da cewa:
“Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Fungzai da Hale da Kubwat da Bwoi da sauran kauyukan yankin Kombun a karamar hukumar Mangu da wasu yankuna a karamar hukumar Riyom, akalla an kashe mutane 130 yayin aka kona gidaje 1000 da kuma majami’u 22 wanda ya shafi kauyuka fiye da 22.”
Kungiyar ta bukaci Kiristoci da kada su gaji wurin rokon Allah ya kawo musu dauki da kuma bai wa mutanen jihar juriya da hakuri.
Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Hare-haren ’Yan Bindiga a jihar Plateau, Mutane Sun Koka
A wani labarin, daga cikin wadanda suka tsira daga hare-haren 'yan bindiga a jihar Plateau sun bayyana yadda suka tsinci kansu.
An kai hare-haren ne a yankuna da dama da ke karamar hukumar Mangu a jihar a ranar Talata 16 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng