“Ina Samun Sama da N860k Duk Watan Duniya”: Inji Matar da Ta Kama Sana’ar Sharan Bola Hannu Bibbiyu

“Ina Samun Sama da N860k Duk Watan Duniya”: Inji Matar da Ta Kama Sana’ar Sharan Bola Hannu Bibbiyu

  • Wata mata da ke sana’ar shara a kasar Burtaniya ta yada wani bidiyon yadda take aikinta a cikin kasar ta turawa
  • A cewarta, tana samun kudin da ya kai £1500 (N860,675.40) duk watan duniya bayan ta biya kudin harajinta a kasar
  • Mutane da yawa a kafar sada zumunta ta TikTok sun ce abin da take samu a kasar ta Burtaniya ya fi albashi a gida

Wata mata da ke zaune a kasar Burtaniya ta ba da mamaki yayin da ta bayyana kudin da take samu a sana’ar shara zalla.

A wani bidiyon da (@akuaserwaa252) ya yada, an ga lokacin da take aikinta na shara a titi, mutane da yawa sun yi mamakin labarin da ta bayar.

Matar da ke samun N860k a sana'ar shara
Sana'ar shara ta yiwa mata wando da riga | Hoto: (@akuaserwaa252
Asali: TikTok

Ta nuna kwarin gwiwa da alfahari da sana’arta

Mutane da yawa ne suka yi ca a karkashin sashen martani na bidiyon, inda da yawa ke cewa, komai kaskancin aikin, ya fi albashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kuma na cewa, za su iya ajiye aikin bankin da suke yi domin kama sharar titi a kasar waje, hakan suka ce ba matsala bane.

Kalli bidiyon:

A kasa ga martanin jama’ar kafar sada zumunta

Yunus Nuhu:

"Irin wakar da na fi so kenan, na gode madam.”

Albie _Nana ama:

"Allah ya albarkaci nemanki.”

user6722823975191:

"Aiki tukutu na ba da nasara. Ki yi kokari ‘yar uwa.”

user75518883288406:

"Ya fi aikin wani da ke dukkan wasu takardu na kwarewa.”

Mo:

"Albashinki ya fi na likitoci da yawa a nan.”

Abuzaa:

"Allah ya albarkaci dukkan iyayen da suka bar kasarsu don yi fafutukar neman abinci ga ahalinsu Allah ya yi albarka mama.”

user7129466672157:

"Ya dai fi zama lakcara, musamman lakcaran kwalejin ilimi.”

Lloyd:

"Ana biyan sama da abin da ake biyan manyan ayyuka da muka sani.”

Kara karanta wannan

Mummunan Karshe: Dan Ta’adda Ya Kai Kansa Ziyara Barzahu Garin Fafatawa da DSS

owurawqe9n6:

"Mafi karancin aiki a kasar waje shine wannan amma kudin da za ta ke samu shine yuro kusan duba daya da dari biyar.”

Kamar almara: Bidiyon kwararriyar mata mai tallan maganin gargajiya akan babur

A wani labarin, wata mata da ke tallan fitaccen maganin gargajiya irin na Yarbawa ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta TikTok.

Wannan ya faru ne bayan da aka yada bidiyon matar a lokacin da take yawo a kan babur tana tallata hajarta.

A bidiyon da @keyrankader_ ya yada, an ga matar ta makare daronta da magani, sannan ta hau babur ba tare da rike daron da ke kanta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.