Kwamishinan Sokoto Ya Yabawa Jami’an ‘Yan Sanda Kan Ƙin Karɓar Cin Hancin N800,000
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto ya yabawa wasu jami'ansu bisa ƙin karɓar cin hancin N800,000 a hannun ɓarayin wayar wutar lantarki
- Waɗanda ake zargi sun yi yunƙurin bai wa 'yan sandan cin hanci domin barinsu su wuce a lokacin da aka kama su da kayan na sata
- Rundunar ‘yan sandan ta kuma gargaɗi ‘yan siyasa da su guji yin duk wasu ayyuka na laifi a yayin bikin ƙaddamar da sabuwar gwamnati mai zuwa
Sokoto - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto Ali Kaigama, ya yabawa wasu jami’an ‘yan sandan jihar bisa ƙin karɓar cin hancin kuɗi har N800,000.
Kwamishinan ya yaba musu ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, Sanusi Abubakar ya fitar ranar Alhamis.
An kama motar cike da wayoyin wuta
Ya ce, a ranar 17 ga watan Mayu, ‘yan sandan da ke sintiri kan titin Sokoto zuwa Birnin Kebbi, sun kama mota ƙirar Sharon shuɗiya mai lamba KSF356 Legas, maƙare da wayoyin wutar lantarki da ake zargin sun sato daga sandunan wutar lantarki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An bayyana sunan mutanen da aka kama da, Rufa’i Sani, Yusha’u Abubakar, da Ahmadu Bello. A yayin da ‘yan sanda ke yi musu tambayoyi, sun yi yunƙurin ba su cin hancin kuɗi N800,000 domin su basu damar wucewa.
Ya ce sai jami'an suka amshi kuɗin a matsayin shaida, sannan suka kamo waɗanda ake zargin tare da motarsu zuwa sashen binciken laifuka na jihar don gudanar da bincike mai zurfi, in ji rahoton Channels TV.
An gargaɗi'yan siyasa dangane da bikin rantsuwa
Rundunar 'yan sandan ta kuma gargaɗi al'ummar jihar game da lalata kayayyakin gwamnati.
Sannan rundunar ta kuma gargaɗi 'yan siyasa dangane da bikin rantsuwa da ke tafe da su kauracewa duk wasu nau'o'in ayyuka na tada zaune tsaye gabanin, lokacin ko kuma bayan rantsar da sabuwar gwamnati.
Sanarwar ta kara da cewa, rundunar za ta cigaba da aikin sintiri da kai samame maɓoyar masu aikata miyagun laifuka har sai mutanen jihar sun samu damar yin barci da idanuwansu kulle.
Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamishinan ya kuma yabawa jami'an ofishin 'yan sanda na ƙaramar hukumar Boɗinga, bisa kama wasu ɓarayin wayar wutar a ranar 13 ga watan Mayun nan da muke ciki.
'Yan sanda sun kama wasu masu satar yara a Neja
A wani labarin kuma, rundunar 'yan sandan jihar Neja ta sanar da kama wasu mutane da ke sace yara da sunan gidan marayu.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ne ya bayyana cewa an kama mutane biyu bayan samun bayanai da jami'ai suka yi kan gidan da ake ajiye yaran.
Asali: Legit.ng